Gobara ta hallaka miji da mata da 'ya'yansu uku

Gobara ta hallaka miji da mata da 'ya'yansu uku Hakkin mallakar hoto MARCO LONGARI
Image caption Gobara ta hallaka miji da mata da 'ya'yansu uku

Wata mummunar gobara a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ta hallaka miji da mata da 'ya'yansu uku ciki har da jariri.

Al'amarin dai ya faru ne a cikin daren Juma'a a lokacin da suke bacci a gidansu da ke garin Bukuru, mai nisan kilo mita 20 daga kudancin Jos babban birnin jihar.

Gobarar ta kone dukkaninsu biyar, in ban da mutum daya daga cikinsu wanda ba ya gida a lokacin da abin ya faru.

Har yanzu ba a san musabbabin gobarar batukna, sai dai hukumomi a kasar sun ce har yanzu suna gudanar da bincike kan ala'amarin.

Labarai masu alaka