2019: An sanya ranar zaben shugaban kasar Nigeria

INEC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption INEC ta fitar da ranar zaben shugaban kasar Najeriya

Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta sanya ranar da za a yi zaben shugaban kasa na shekarar 2019, inda za a yi zaben nan da kwana 433 masu zuwa.

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019 ne za a yi zaben shugaban kasar da 'yan majalisar tarayya.

Yayin da ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2019 za a yi zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha, da kuma zaben shugabannin kananan hukumomin babban birnin Najeriya Abuja.

Yakubu ya bayar da sanarwar ne ranar Juma'a a wani taro da huhumar ta gabatar a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

"Duk wadanda suka halartaci taron nan ya kamata su san cewa daga yau (Juma'a) saura kwana 434 a gudanar da babban zaben shekarar 2019, wato ranar 16 ga watan Fabrairu inda za a fara da zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya," in ji shi.

Ya kara da cewa, sababbin masu kada kuri'a kimanin 3,630,529 aka yi rijista, kuma za a ci gaba da yin rijistar har zuwa kwana 60 kafin babban zaben.

A kalla jam'iyyu 67 ne suka nuna sha'awarsu ta shiga zaben, har ila yau hukumar ta karbi takardar masu neman yin rijista fiye da 120 daga kungiyoyin siyasa da suke neman a yi musu rijista a matsayin jam'iyya.