Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari

buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/ Presidency
Image caption Shugaban ya kai ziyara jihar Kano ne a ranar Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce jama'ar jihar Kano sun nuna wa jama'ar kudancin kasar cewa har yanzu yana da gata.

Shugaban ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake jawabi yayin da yake ziyarar kwana biyu.

Ya ce sun yi yakin neman zabe a shekarar 2015 a kan abubuwa uku wato: matsalar tsaro da batun tattalin arziki da kuma matsalar cin hanci da karbar rashawa.

Shugaba Buhari ya ce abin da ya fi ba shi wahala a tsawon mulkinsa na fiye da shekara biyu "shi ne hana yaki da cin hanci da rashawa."

Daga nan ya ba da labarin yadda ya yi yaki da cin hanci da rashawa yayin da yake jagorantar kasar a karkarshin mulkin soja wato a tsakanin shekarun 1983 zuwa 1985.

Ya ce yanzu ba zai iya yakar cin hanci da irin wancan tsohon salon da ya yi amfani da shi ba a wancan lokacin.

Har ila yau shugaban ya tabo batun yadda ya kwashe kimanin shekara uku a tsare bayan da aka masa juyin mulki.

Shugaban ya ce an sallame shi ne bayan da aka fahimci bai ci amana ba. "Allah Ya sa ba a same da cin amana ba har yanzu."

Hakazalika shugaban ya ba da labarin yadda hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati (EFCC) ta kai samame gidan wani babban alkalin kotun kolin kasar.

"An samu kudin kasashen waje da kuma fasfo na tafiye-tafiyen diflomasiyya guda hudu," in ji shugaban.

Kamar yadda ya saba, shugaban ya soki gwamnatocin da suka gabace shi da kin yin tanadin yayin da farashin mai yake da tsada a kasuwannin duniya.

Har ila yau, yayin jawabin shugaban ya taba nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta cimma a bangaren tsaro da kuma aikin gona.

Labarai masu alaka