Kashi 70 na daliban arewa a jahilai suke gama makaranta - Masani

Students Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masanin ya bukaci kawar da cin hanci da rashawa a harkar ba da ilmi a Najeriya

Wani masani daga Jami'ar Alkalam a Najeriya ya bayyana fargaba kan karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar, a cewarsa kusan duk 'yan arewa sun kwanta sun zuba ido "ilmi ya gyara kansa".

Gogaggen malamin jami'ar wanda ya gudanar da bincike na kashin kansa a makarantu daban-daban cikin yankin ya ce ya yi matukar kaduwa da abin da idonsa ya gani.

A cewar Dr. Aliyu Muri: "to kuma abin kusan kullum sai kara ci gaba yake yi. Kamar ciwo ne, kullum ba a magance shi ba, yana kara hauhawa ne".

"Ta kai (matsayin) yanzu yaranmu hakan nan suke gama karatu, wadanda suke gama firamare, su gama hakan nan, wadanda suke gama sakandare, su gama haka nan (ba tare da wani ilmi ba)," in ji shi.

Ya ce binciken da wata kungiya ta gudanar inda ta gano cewa kashi 70% na yaran da suke gama makarantu a arewa, suna gamawa jahilai, shi ne dugunzuma shi kuma ya yi masa kaimin gudanar da nasa bincike.

Dr. Muri ya ce ya ziyarci makarantu da dama a yankunan karkara da maraya, kuma akasari makarantun karkara da ya halarta ya gano matsanancin karanci na malaman da ke koyarwa.

"A karkara za ka iske akwai sakandaren da ke da malamai guda biyar kawai kuma ana koyar da kimiyya da fasaha. Babu malamin turanci ballantana a yi maganar lissafi."

Ya ce ya ziyarci wata makaranta da ya shiga ajin karshe na sakandare, wadda da kyar aka iya samun wani yaro da ya tashi ya iya karanta kalmar "Allahu" da ke rubuce a kan allo.

"Kuma wadannan yaran, idan sun gama za a ce maka duk sun yi WAEC. Sun ci jarrabawarsu ta gama makaranta, sannan kuma irinsu ake kwasa a shigar da cikin manyan makarantunmu. Ina za mu sa kanmu?" Ya tambaya.

Dr. Aliyu Muri ya alakanta rashin kulawar da ake bai wa bangaren ilmi, da zama ummul aba'isin wannan matsala.

A cewarsa: "Za ka iske makaranta mai (dalibi) dubu biyar, dubu shida. Akwai wadda aka fada min tana da yaro dubu goma sha uku.

Ya yi tambayar ko yaya arewa za ta yi da kanta idan wadannan yara suka taso daga nan zuwa shekara, musammam idan ka yi la'akari da irin yawansu a kan tituna idan sun dawo bayan an tashe su?

Labarai masu alaka