An bukaci duniya ta amince da kafa kasar Falasdin

Middle East Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Rikici ya barke a garin Nablus da ke Gabar Yamma da Jordan ranar Asabar

Ministocin harkokin waje ashirin da biyu da ke wakiltar kasashen Larabawa sun nemi Amurka ta janye matakin da ta dauka na daukar Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawan ta ce shawarar amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, tana cike da hatsari.

Matakin dai ya kawo karshen kasancewar Amurka 'yar ba-ruwanmu a daya daga cikin batutuwa mafi zafi a Gabas ta Tsakiya.

Ministocin wajen kasashen Larabawa a yanzu sun ce hakan na nufin ba a iya dogaro da Amurka a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya a yankin ba.

Sanarwar kasashen 22, wadda ta kunshi manyan kawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya, ta zo ne bayan hargitsi a kwana na uku da jerin zanga-zanga a Gabar Yamma da kuma Zirin Gaza.

A wata sanarwa bayan wani taron gaggawa a birnin Alkahira, ministocin sun ce matakini, keta dokar kasashen duniya ce kuma yana barazanar tsunduma Gabas ta Tsakiya cikin rikici.

Sun kuma yi kira ga kasashen duniya su amince da kasar Falasdin da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta.

Ministan wajen Lebanon, Gebran Bassil ya ma yi kira ga kasashen Larabawa su yi tunanin kakaba wa Amurka takunkuman karya tattalin arziki don hana ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Kudus daga Tel Aviv.

Labarai masu alaka