Birnin Kudus: An tarwatsa masu zanga-zanga a Lebanon

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jami'an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar a birnin Beirut

An yi arangama yayin wata zanga-zangar adawa da matakin Trump kan birnin Kudus a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Beirut na kasar Lebanon.

A makon jiya ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila da kuma mayar da ofishin jakadancin kasar zuwa can.

Yayin zanga-zangar jami'an tsaron Lebanon sun rika watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi a arewacin birnin Beirut.

A daren ranar Asabar ne Kungiyar Kasashen Larabawa ta yi Allah-wadai da matakin Shugaba Trump.

Kungiyar ta ce daga yanzu bai kamata a dogara ga Amurka wajen samar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ba.

Masu zanga-zangar sun rika jefa da duwatsu da cinna wuta a kan tituna a kusa da ofishin jakadancin da ke unguwar Awkar.

Wadansu kafafen yada labarai sun ce masu zanga-zangar sun yi kokarin kutsa kai cikin ofishin jakadancin.

Masu zangar-zangar wadanda suke sanye da bakaken kaya sun rika rera wakokin Allah-wadai da Shugaba Trump.

Akwai dubban Falasdinawa 'yan gudun hijira da ke zaune a kasar Lebanon.

Tun bayan da Shugaba Trump ya sanar da daukar matakin ne aka rika samun zanga-zangar adawa da matakin a birnin Kudus da kuma sauran biranen duniya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugabannin duniya sun yi wa Trump kashedi kan Kudus