Ana tuhumar mata 24 da laifin sanya wando a Sudan

Sudanese women in Khartoum Hakkin mallakar hoto Getty Images

An gurfanar da mata 24 bisa tuhumarsu da nuna rashin da'a bayan sun sanya wanduna a wani taron liyafa a kusa da birnin Khartoum na kasar Sudan.

'Yan sanda sun cafke su ne bayan wani sameme da suka kai yayin taron liyafar a ranar Laraba.

Matan da ake tuhuma za su iya fuskantar hukuncin bulala 40 da kuma tara.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce dubban mata ne ake wa bulala duk shekara a kasar bayan an same su da laifin rashin kamun kai.

Har ila yau sun ce dokar hana mata sanya wando da kuma guntun siket tana shafar Kiristocin kasar wadanda su ne tsiraru.

Galibin al'ummar Sudan Musulmi ne kuma mata a kasar suna sanya dogayen tufafi ne bisa al'ada.

Karanta wadansu karin labarai:

Labarai masu alaka