Ronaldo ya ce babu dan kwallon da ya fi shi a tarihi

Ronaldo ya lashe gasar Ballon d'Or karo na biyar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ya lashe gasar Ballon d'Or karo na biyar a bana

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce shi ne "fitaccen dan kwallo a tarihi", bayan da ya lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya, wato Ballon d'Or karo na biyar.

Ronaldo ya lashe kyautar karo na biyar jere, inda ya yi kankankan da dan kwallon Barcelona Lionel Messi, ya kuma ce bai yi amannar cewa akwai wani dan wasa da ya fi shi ba.

"Babu dan wasa sama da ni. Ina buga tamaula sosai, ina da sauri, ina da karfi, ina buga kwallo da kai, na ci kwallaye, na taimaka an ci, akwai mutanen da suka fi son Neymar ko Messi, amma na fada babu wanda yake da irin wadannan abubuwan fiye da ni," in ji dan kwallon.

Ya kara da cewa," Babu wanda ya lashe kyautuka iri daban-daban kamar ni. Ba ina magana a kan kyautar Ballon d'Or kawai ba ne."

Karanta wadansu karin labarai:

Labarai masu alaka