Yara dubu 170 na amfani da intanet a kullum

Lionel Messi da wasu yara sanye da rigar UNICEF Hakkin mallakar hoto Getty Images

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya yi kira ga kwararru a fannin sadarwa ta zamani da su dauki kwararan matakan kare kananan yaran da ke amfani da kafar sadarwa ta internet.

UNICEF, ya ce a kowacce rana ana samun sama da yara dubu dari da saba'in da suka fara amfani da internet a duniya.

Asusun ya ce, a dai-dai lokacin da ake kara samun karuwar yaran da ke amfani da intanet din, akwai bukatar fito da sabbin matakan kare masu amfani da ita.

A karshe UNICEF, ya bada shawarar a duk lokacin da yara su ka yi amfani da intanet, ya na da kyau a rinka sakaya sunayensu.