Yadda fyade da kisan 'yar shekara 6 ya harzuka India

Locals carry the body of the six-year-old who was brutally raped and murdered Hakkin mallakar hoto Manoj Dhaka
Image caption An yi wa 'yar shekara shidan fyade tare da kashe ta

'Yan sanda a Indiya suna yi wa mutane da dama tambayoyi dangane da fyade na rashin imani da kuma kisan gillan da aka yi wa wata yarinya 'yar shekara shida a jihar Haryana da ke arewacin kasar.

An tsinci gawarta ranar Lahadi kusa da gidansu inda aka yi zargin cewa an sace ta cikin dare ranar 8 ga watan Disamba.

Irin mummunan ciwon da aka yi wa yarinyar lokacin fyaden ya bata wa Indiyawa rai matuka inda mafi yawa daga cikinsu suke alakanta batun da fyaden cikin bas da aka yi a birnin Delhi a shekarar 2012 wanda ya harzuka mutane matuka.

Mahaifiyar yarinyar ta shaida wa BBC cewa suna bukatar a hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

"Yanzu an samu sa'o'i 24 bayan aikata wanna aikin, kuma kawo yanzu 'yan sanda ba su kama kowa ba," in ji ta.

'Yan sanda sun kama 'yan uwan mijinta uku domin yi musu tambayoyi, amma har yanzu ba a tsare kowa ba. Sai dai kuma da haka ba a bayar da karin bayanai ba.

Gwamnatin kasar ta nada wani kwamitin masu bincike yayin da mutane suke kara matsa mata lamba domin ta kama wadanada suka aikata danyen aikin. Mutane ciki har da masu fafatuka da shugabannin siyasa daga gundumar sun hallara a kauyen domin su kaddamar da zanga-zanga.

Iyayen yarinyar suna bukatar cewa 'yan sandan gwamnatin tarayyar kasar su gudanar da bincike kan lamarin, suna masu cewa ba su amince da 'yan sandan jihar ba.

Mahaifin yarinyar, wani mai sana'ar sayar da tsumokara, ya ce ya fita aiki ne a daren da aka saci 'yarsa.

A lokacin da matarsa ta tashi washe gari, ya ce , ta fahimci cewa 'yarsu ta bata. Iyayen yarinyar suna da wasu 'ya'ya uku - yara biyu da 'ya mace daya.

Hakkin mallakar hoto Manoj Dhaka
Image caption Daga farko dai iyayen yarinyar sun ki su kona gawarta har sai an yi kame

Iyayen suna zama ne a wani fili tare da wasu iyalai hudu a garin Haryana. 'Yan sanda suna zargin cewa wadanda suka yi wa yarinyar fyade tare da kashe ta za su iya kasancewa sun zo ne daga unguwar marasa galihu da ke kusa da inda iyayen suke.

Daga farko iyayen yarinyar sun ki su kona gawarta har sai an kama wadanda suka kashe ta. An ci gaba da jana'izarta ne kawai bayan 'yan sanda sun tabbatar musu da cewa za su yi kame nan ba da jimawa ba.

Sun bai wa 'yan sanda wa'adi - karfe 11 na safiyar Laraba - na su yi kame. Idan hakan bai faru ba, sun yi barazanar zuzuta zanga-zangar.

Labarai masu alaka