Hazo ya hana jirage tashi a Nigeria

Hazo ya hana daruruwar mutane tafiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hazo ya hana daruruwar mutane tafiya

Hazo ya sa an soke tashin gomman jirage a Najeriya, lamarin da ya sa matafiya da dama suka kasa samun jirage.

An soke akalla tashin jirage 20 a manyan filayen tashin jiragen sama a fadin Najeriya lamarin da ya sa daruruwan matafiya suka shiga wani hali na rashin tabbas.

Hazon dai ya sa ba a iya gani fiye da mita 400 a wurare da dama a Najeriya, yayin da ake bukatar iya gani na mita 800 kafin jirgi ya tashi ko kuma ya sauka.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi gargadin cewa za a yi hazo a sararin samaniyar jihohin da ke tsakiyar Najeriya, ranar Litinin.

Amfani da jiragen sama dai wata hanya ce wadda wasu 'yan Najeriya ke bi wajen zirga-zirgar yau da kullum.

Labarai masu alaka