'Yan Kannywood sun yi jimamin shekara uku da mutuwar Dan Ibro

Ibro ya fito a fim din Babban Direba na Ilyas Tantiri dab da rasuwarsa Hakkin mallakar hoto Instagram/Abdul Ilyas Tantiri
Image caption Ibro ya fito a fim din Babban Direba na Ilyas Tantiri dab da rasuwarsa

Masu ruwa da tsaki a fina-finan Kannywood sun tuna da mutuwar fitaccen dan wasan barkwancin nan Rabilu Musa (Dan Ibro), shekara uku bayan rasuwarsa.

Dan Ibro ya rasu ne ranar goma ga watan Disambar shekarar 2014 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya bayan ya yi fama da ciwon koda.

Wasu daga cikin masu harkokin fim sun bayyana irin kusancin da ke tsakaninsu da kuma kyawawan halayensa.

Darakta kuma jarumin fina-finai Falalu Dorayi ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa: "Shekara uku kenan, 10th December 2014 da rasa abokin neman halak. Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un.

"Allah ya yi maka Rahma Alhaji Rabilu Musa Ibro. Allah ya sanya haske da ni'ima a kabarinka. Allah yai mana rahma baki daya. Allahu akbar. Rashin da babu madadinsa."

Shi ma Ilyas Abdulmumini Tantiri, wanda fim dinsa shi ne na karshe da Dan Ibro ya fito a ciki kafin ya rasu, ya ce "Alhaji Rabilu Musa (Ibro) mutum ne sak, mai kishin sana'arsa da abokan sana'a.Bai fiye magana ba a inda babu ruwansa, mai fadar gaskiya ne ba tare da tsoro ba. Kuma yana da halacci ga wanda ya yi masa halacci. Allah ka jikan Rabilu, ka yafe masa kura kuransa.Amin".

Hakkin mallakar hoto InSTAGRAM/ALI NUHU
Image caption Ali Nuhu da Dan Ibro sun fito tare a fina-finai da dama
Hakkin mallakar hoto InSTAGRAM/Falalu Dora
Image caption Dan Ibro ya sha yin kalamai irin na siyasa a fina-finansa

Shi kuwa jarumi Ali Nuhu wallafa wani sashe na fim din da ya fito tare da Dan Ibro ya yi a shafinsa na Instagram, kana ya yi sharhi a karkashinsa inda ya ce: " Sarki, sarki ne har abada. Muna kewarka, Chairman".

Labarai masu alaka