Za a kyale 'yan Saudiyya zuwa kallo a sinima

A Saudi woman takes a selfie with person dressed as the Beast from Disney's 2017 Beauty And The Beast film at a Comic Con Arabia event Riyadh on 25 November 2017 Hakkin mallakar hoto AFP

Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta dage haramcin da ta sanya kan zuwa sinima fiye da shekara 30 da suka wuce.

Ma'aikatar al'adu da watsa labaran kasar ta ce za ta soma bayar da lasisi nan take ga masu gidan sinima domin su fara budewa a watan Maris na shekarar 2018.

Matakin na cikin sauye-sayen da mai jiran gadon sarautar Saudiyya Yarima Mohammed bin Salman yake gudanarwa zuwa shekarar 2030.

Kasar ta Saudiyya, wacce ke bin tafarkin Musulinci sau da kafa, tana da gidajen sinima a shekarun 1970 amma Malaman addini sun sanya hukumomi rufe su.

A watan Janairun da ya gabata, an ambato Babban Limamin Masallatan Harami, Sheikh Abdul Aziz a--Sheikh yana yin gargadi kan illolin sinima, yana mai cewa za su bata tarbiyyar 'yan kasar.

'Ya'yan gidan sarautar Saudiyya da kuma Malaman addini na bin mazahabin Sunnah.

Wata sanarwa da ma'aikatar al'adu ta fitar ranar Litinin ta ce an dauki mataki bai wa masu gidan sinima lasisi ne saboda yana da muhimmanci wurin "saye-sauyen da gwamnati ke yi domin karfafa gwiwar samar da budaddiya kuma cikakkiyar al'ada ga 'yan kasar".

"Hakan wata hanya ce ta bunkasa al'ada a fannin tattalin arziki a wannan kasar," in ji ministan Al'adu Awwad Alawwad.

"Bude sinima zai zama wata hanyar bunkasa tattalin arziki da; idan aka fadada al'adu za a samar da sabbin ayyuka da horaswa, da kuma bunkasa hanyoyin samar da nishadi a wannan Daula."

Wasu mawakan hip hop irin su Nelly da Ceb Khaled za su yi waka a birnin Jedda ranar Alhamis, ko da yake maza ne kawai za su halarci wurin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hiba Tawaji ce mawakiya ta farko da ta rera waka a kasar Saudiyya a makon jiya

Labarai masu alaka