An kai harin bama-bamai a Amurka

Police at Port Authority Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan sanda a birnin New York City na Amurka sun ce an tsare wani mutum sakamakon tashin wasu abubuwan fashewa a tashar jirgin kasa da ke yankin Manhattan mai cike da hada-hada.

Abubuwan sun fashe ne a kusa da Times Square.

Ma'aikatan kwana-kwana sun ce mutum hudu sun ji rauni, ko da yake ba masu muni ba ne.

Magaji birnin New York Bill de Blasio ya ce " 'Yan ta'adda ba za su taba yin nasara a kanmu ba. Mu ne muyanen birnin New York".

An bayyana sunansa maharin da Akayed Ullah, mai shekara 27.

'Yan sanda sun ce Ullah ma ya ji rauni.

Wasu kafofin watsa labaran Amurka sun ambato jami'an da ba su bayyana sunayensu ba na cewa mutumin ya tayar da bam din da ke jikinsa a lokacin da ake tururuwar zuwa aiki.

Mai magana da yawun fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta ce an shaida wa Shugaba Donald Trump hfaruwar lamarin.

Labarai masu alaka