Muhimman abubuwa da suka faru a duniya a shekarar 2017

Yayin da shekarar 2017 ke karewa, al'ummar duniya ba za ta manta da wasu muhimman abubuwan da suka faru ba a shekarar wadanda su ka fi jan hankalin jama'a.

Guterres ya fara aiki a matsayin sakataren MDD

Kusan za a iya cewa an fara shekarar 2017 da kafa tarihi a Majalisar Dinkin Duniya inda a farkon watan Janairun shekarar Antonio Guterres ya kama aiki a matsayin sabon sakatare Janar na Majalisar.

Mr Guterres wanda tsohon Firai ministan Portugal ne, ya jaddada cewa manufar kafa Majalisar ita ce kawo karshen yake-yake a duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Guterres ya jagoranci hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD

Da yake jawabi, sabon sakataren ya ce tilas ne a yi gyare-gyare a Majalisar domin aiki kamar yadda ake bukata.

An rantsar da Donald Trump

Wani muhimman abu da ya ja hankalin jama'ar duniya a 2017 shi ne rantsar da Donald Trump ranar 20 ga watan Janairun shekarar a matsayin shugaban Amurka na 45.

Mr Trump wanda ya rika magana cikin hasala a lokacin rantsar da shi, ya yi alkawarin mayar da iko hannun jama'a daga Washington.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Trump a lokacin da yake rantsuwa don kama aiki a matsayin shugaban Amurka

Cincirindon jama'ar da suka taru don shaida bikin rantsuwar a gaban ginin majalisun Amurka Capitol Hill sun rika yi masa sowa da tafi.

Tsofaffin shugabannin Amurkar da suka hada da Bush karami da Jimmy Carter da Bill Clinton da kuma shugaba mai barin gado Barrack Obama duk sun halarci bikin rantsuwar.

Kazalika Hillary Clinton wacce ta sha kaye a hannun Mista Trump ita ma ta halarta.

An rantsar da Adama Barrow shugaban Gambia

Gabanin a rantsar da shugaban Amurka sai da duniya ta shaida rantsar da Mr Adama Barrow ranar 19 ga watan Janairun 2017 a matsayin sabon shugaban kasar Gambia.

An dai gudanar da bukin rantsarwar ne a ofishin jakadancin kasar da ke Senegal.

Mista Barrow ya je Senegal ne bayan yunkurin da kungiyar Ecowas ta yi na ganin Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin ruwan-sanyi ya gagara.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adama Barrow ya samu goyon bayan matasa sosai

Tun da farko Yahya Jammeh ya amince da shan kaye ya kuma taya Mista Barrow murna, amma daga bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.

Trump yasa hannu a dokar hana wasu Musulmi shiga Amurka

Wani al'amari da har ila yau ya ja hankalin jama'a a duniya shi ne sanarwar da Shugaba Donald Trump ya yi na daukar wasu matakai na hana Musulmi 'yan wasu kasashe shiga Amurka.

Matakin da shugaba Trump ya sanar a watan Janairu dai ya janyo suka tare da zanga-zanga a ciki da wajen Amurkar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na duniya kan matakin da Trump ya dauka

Daga bisani kuma shugaba Donald Trump ya kori Antoni Janar din kasar ta rikon-kwarya Sally Yates bayan ta ki goyon bayan shirinsa na korar 'yan gudun hijira da Musulmi daga kasar.

An kai hari a Majalisar Dokokin Burtaniya.

A kalla mutane hudu da suka hada da wani jami'in dan sanda suka mutu yayin da wasu mutum 20 suka jikkata a harin ta'addanci da aka kai harabar Majalisar Dokokin Burtaniya a watan Maris .

Harin dai ya faru ne a dai-dai lokacin da majalisar dokokin Scotland ke mahawara kan yiwuwar gudanar da kuri'ar raba gardama kan zama ko barin Burtaniya.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda da Jami'an agajin gaggawa sun killace wurin da aka kai harin

Firai ministar Burtaniya Theresa May ta yi Allah-wadai da harin inda kuma ta yabawa kokarin 'yan sanda yayin harin.

Zaftarewar laka ta haddasa mutuwa a Colombia

An shiga wani yanayi na jimami bayan da aka ba da rahoton mutuwar mutum 250 sakamakon zaftarewar laka a birnin Mocoa na kasar Colombia.

Kimanin wasu mutum 300 kuma sun bace fiye da 40 a cikinsu kananan yara ne.

Mamakon ruwan sama ne ya haifar da ambaliyar ruwa a birnin Mocoa da ke kudu maso yammacin kasar inda tabo da duwatsu suka yi awon gaba da daukacin yankin abin da ya tilastawa mutane tserewa.

Macron ya zama shugaban kasar Faransa

Duniya ba za ta manta nasarar da Mr Emmanuel Macron dan takara mai matsakaicin ra'ayi ya yi na lashe zaben shugaban kasar Faransa a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar.

Mr. Macron mai shekaru 39 ya kayar da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ms Le Pen din dai ta taya sabon shugaban murna, jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben.

Ya kasance shugaban kasar Faransa mafi karancin shekaru da aka zaba kuma na farko da baya cikin manyan jam'iyyun kasar guda biyu.

Koriya ta Kudu ta yi sabon shugaba

Shi ma Moon Jae ya kafa tarihi inda a ranar 9 ga watan Maris aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Koriya ta Kudu.

Sabon shugaban dai ya maye gurbin shugaba Park Geun-hye wacce Majalisar dokokin Korea ta Kudu ta tsige bisa zargin aikata cin hanci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mr Moon ya ce a shirye yake ya je Koriya ta Arewa matukar yanayin da ake ciki ya inganta

Gabanin rantsar da shi sabon shugaban kasar ya shaida wa al'ummar Koriya ta Kudu cewa yana son ganin kowa yana tafiyar da al'amuransa a kasar ba tare da tsangwama ba.

Duniya ta yi caa akan Trump saboda ficewa daga yarjejeniyar Paris

Matakin da shugaban Amurka Donald ya sanar ranar 1 ga watan Yuni 2017 na ficewar Amurkar daga yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a Paris ya ja hankalin jama'ar duniya.

Kasashen da dama ciki har da Birtaniya da Faransa sun bayyana takaicinsu kan shawarar Trump ta ficewa daga yarjejeniyar inda kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana ranar a matsayin ranar bakin ciki ga duniya.

Shi dai shugaba Trump ya ce yarjejeniyar ba ta da wani tasiri kan yanayi kuma tana kuntatawa Amurkawa ne saboda shimfida sharudda masu tsauri fiye da kasashen da suka fi gurbata muhalli.

Kasashen Larabawa sun juyawa Qatar baya

Rikicin da ake fama da shi a wasu kasashen Larabawa ya dauki sabon salo bayan da a watan Yunin 2017 Saudiyya da Bahrain da Hadaddiyar daular Larabawa da Masar suka katse huldar diplomasiyya da Qatar.

Saudiyya ta rufe iyakokinta na kasa da sama da kuma ruwa da kasar Qatar bayan ta zargi kasar da marawa ta'addanci baya.

A nata bagaren dai kasar Qatar din ta yi ta musanta zargin da ake yi mata na tallafawa masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Birtaniya: Theresa May ta kasa samun rinjaye

Duniya ta yi mamakin sauye-sauyen da ake gani a siyasar Burtaniya bayan da Firai Minista Theresa May ta rasa samun rinjayen da ta ke bukata don kama gwamnati bayan samun sakamakon da yawa daga cikin kujerun majalisar dokokin Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Misis May ta ce Britaniya na bukatar yanayi na tabbas da zaman lafiya da shugabanci

A zaben da aka gudanar a watan Yunin 2017, Jam'iyyar da ta samu kujerun majalisar dokoki 326 cikin 650 da ake da su a kasar ne ta kafa gwamnati.

Hassan Rouhani ya samu yin tazarce

Masu sharhi da dama ba su yi mamakin nasarar da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya samu na lashe zaben kasar karo na biyu ba.

Sai dai babban mai hamayya da shi Ebrahim Raisi mai tsattsauran ra'ayi ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben.

Hakkin mallakar hoto EBRAHIM NOROOZI
Image caption Mr Rouhani ya goyi bayan yarjejeniyar da kasar sa ta kulla da kasashen yamma domin ta rage kera makamashin nukiliya

Mr Rouhani shi ne mutumin da ke da matsakaicin ra'ayi wanda ya amince da yarjejeniyar da kasarsa ta kulla da kasashen yammacin duniya domin ta rage kera makamashin nukiliya.

Al'ummar Saliyo sun gamu da ibtila'i

Kasar Saliyo ta tsinci kanta cikin wani mummunan bala'i inda kimanin mutum 800 suka mutu yayin da kimanin mutum 600 suka bace, kuma a kalla mutum 7,000 suka rasa muhallansu.

Wannan al'amari dai ya abku ne bayan makonni da aka yi ana sheka ruwan sama inda tsaunin Sugar Loaf daya rufto ya murkushe gidajen al'ummar da ke zaune a wajen.

Hakkin mallakar hoto OLIVIA ACLAND
Image caption An yi jana'izar daruruwan mutunen da suka mutu

Ruwan sama ya rika tunkodo laka da duwatsu daga saman tsaunin inda ya rushe gidaje a wasu yankuna biyu na Kamayama da Kaningo.

Zaben Shugaban kasar Kenya ya bar baya da kura

Kusan za a iya cewa murna ta koma ciki a farkon watan Satumban 2017 bayan da kotun kolin kasar Kenya ta soke sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Agusta.

Kotun ta ce ta gano cewa an tafka kura-kurai a zaben da aka sanar da Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe kuma ta ba da umarnin a sake sabon zabe cikin kwanaki 60.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daruruwan jama'a ne suka je rumfunar zaben don kada kuri'a

Sai dai a ranar 30 ga watan Satumba 2017 an sake ayyana Shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben mai cike da ce-ce-ku-ce bayan da Jagoran 'yan Adawa Raila Odinga ya janye daga takarar.

Myanmar: 'Ana yi wa Musulmin Rohingya kisan kare-dangi'

Wani abu da ya ja hakalin duniya a 2017 shi ne irin kisa da ya yi kama da na kare-dangi da aka yi wa Musulmai 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da musulmai na kabilar Rohingya 300,000 ne suka tsere kasar Bangladesh tun bayan fara rikicin a watan Agustan 2017.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kiyasi na baya-bayan nan ya nuna mutane 313,000 suka tsere daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh.

A nasu bangaren sojojin kasar sun ce suna kai hare-hare ne kan mayakan sa-kai na Rohingya kuma sun musanta aikata ba daidai ba da kisan fararen hula.

Ayatollah Khamenei na Iran 'Hitler' ne - Yariman Saudiyya

Kusan za a iya cewa dangantaka tsakanin kasar Saudiyya da Iran ba ta sauya ba illa ma dai ta kara tabarbarewa ne a 2017.

A watan Nuwamba ne Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman, ya bayyana jagoran addinin Iran a matsayin sabon Hitler na Gabas ta Tsakiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yerima Salman matashi ne dan shekara 32 wanda mahaifinsa ya daukaka.

Saudiyya da Iran dai manyan abokan fada ne kuma a baya-bayan nan ana samun ci gaba da nuna yatsa tsakaninsu.

Cacar baki tsakanin Amurka da Korea Ta Arewa

An ci gaba da cacar baki da kuma tada jijiyar wuyar tsakanin Amurka da Koriya ta arewa kan gwajin makaman nukiliya da na kare-dangi da Koriyar ta yi duk da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata.

Lamarin dai ya sa a watan Satumbar 2017 Shugaba Donald Trump ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa Amurka za ta lalata Koriya Ta Arewa idan har tura ta kai bango don ta kare kanta da kawayenta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Amurka da takwaransa na Koriya Ta Arewa ba sa ga maciji a kan shirin kasar na nukiliya

Sai dai a martanin da ta mayar Koriya ta Arewar ta ce haushin kare kawai Trump ya ke yi.

Ballewar yankin Catalonia daga Spaniya na daukar sabon salo

An dai yi ta kai ruwa rana bayan da Majalisar dokokin yankin Catalonia na Spaniya ta kada kuri'ar ballewa daga kasar baki daya domin kafa kasarsu.

Rikici ya barke ne lokacin da jama'ar yankin suka kada kuri'a mai cike da rudani a farkon watan Oktoba inda suka amince da kafa kasar su mai cin gashin kanta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya bayan ballewar yankin sun taru a gaban majalisar a lokacin da ake kada kuri'ar

Fira ministan Spaniya Mariano Rajoy ya ce ko alama gwamnatinsu ba za ta lamunci abin da ta kira yaudara da bata suna ba dangane da ballewar yankin Cataloniya.

Bala'in girgizar kasa a Mexico

Al'ummar Kasar Mexico sun yi jamami na mutuwar fiye da mutum 200 a wata mummunar girgizar kasa ta faru a tsakiyar birnin Mexico a watan Satumba.

Girgizar wadda ta kai karfin lamba 7.1 a ma'aunin girgizar kasa ta rushe gomman gine-gine a babban birnin kasar wato Mexico City.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu aikin agaji da 'yan sa-kaisun yi kokarin gano masu rai a karkashin wata gada da ta ruguje

Bala'in ya auku ne yayin da mutane da dama suka shiga wani atisaye na yadda ya kamata a yi a lokacin da girgizar kasa ta auku, daidai shekara 32 da ta wuce lokacin da wata girgizar ta hallaka dubban mutane.

Zanga-zangar neman ballewa daga Kamaru

Masu sharhi na ganin har yanzu da sauran rina a kaba game da yunkurin wasu al'umma a yankin kudu maso yammacin Kamaru mai amfani da harshen Ingilishi na neman ballewa daga kasar.

An dade ana takun saka tsakanin gwamnatin kasar da mutanen kudancin kasar da ke amfani da harshen Ingilishi kan abin da masu fafatuka suka kira rashin yi wa yankin adalci.

Hakkin mallakar hoto STRINGER
Image caption Har ma a birnin Bamenda da ke Kamaru, masu fafatuka sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da wariyar da suka ce ana yi wa 'yan kasar masu Ingilishi

Shugaba Paul Biya dai ya bayar da umarnin shirya sojoji domin kare kasar tare da tabbatar da tsaro ga dukkan 'yan kasar ma su mutunta doka.

Saudiyya ta sakarwa mata a kasar mara

Wasu muhimman batutuwa da dama sun faru a kasar Saudiyya a shekarar 2017 wadanda kuma ba za a taba mantawa da su ba.

A karon farko dai kasar Saudiyya ta sakar wa matan kasar mara inda ta sanar da fara barin mata zuwa filayen wasa domin kallon wasannin da kuma janye dokar hana mata tuka mota a kasar.

Kazalika, an kada kuri'ar amincewa da ba mata damar yin fatawar addini.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matan Saudiyya sun dade suna fafutikar neman 'yancin walwala

Wadannan matakai da Sarki Salman na Saudiyyar ya dauka ya jawowa kasar yabo a kasashen yammacin duniya.

Somaliya: Har yanzu 'yan ta'adda na cin karen su ba babbaka

Duk da cewa an sha fama da hare hare ta'addanci a kasar Somaliya, mummunar harin da aka kai a watan Oktoba zai dade cikin zukatan al'ummar kasar.

Hukumomi sun ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar harin bam din da aka kai birnin Mogadishu ya kai 358.

Akwai dakarun kungiyar Tarayyar Afirka 22,000 a kasar wadanda suke taimaka wa gwamnati wajen sake kwato yankunan da ke hannun Al-Shabab, wadanda suke da tasiri a yankunan karkarar kudancin kasar.

Zimbabwe: Bayan shekara 37 akan mulki, Mugabe ya yi murubus

Mai yiwuwa za a iya cewa duniya za ta dade tana tuna abubuwan da suka wakana wadanda suka tilasta wa shugaban Zimbabwe Robert Mugabe murabus bayan ya kwashe shekaru 37 akan karagar mulki.

Mista Mugabe mai shekara 93 da farko ya ki yarda ya yi murabus duk da kwace iko da sojoji suka yi na tsawon mako guda da kuma zanga-zangar adawa da shi da aka rika yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mugabe ya bai wa matarsa Grace goyon bayan zama mataimakiyar shugaba

Daga bisani ne kuma aka rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe a wani biki da dumbin jama'a suka taru a filin wasa na Harare, babban birnin kasar.

Taron jam'iyyar Kwaminis a China

A watan Oktoba ne aka gudanar da babban taron jam'iyyar kwaminis mai mulkin China karo na 19 .

A taron da aka saba yi kowacce shekara biyar manyan shugabannin jam'iyyar sun yanke hukunci kan mukaman gwamnati.

Shugaba Xi Jinping ya yi ta zarce a matsayin shugaban jam'iyyar inda kuma aka samu sauye-sauye a shugabancin jam'iyyar na wasu da suka yi ritaya.

An gudanar da wannan taron ne yayin da Chinan ke kara samun bunkasar tattalin arziki da kuma fada a ji a siyasar duniya.

Ko me ya sa aka kama ministocin Saudiyya?

Tun bayan kama wasu ministoci hudu da kuma Yarimomin gidan sarautar Saudiyya 11 kan zargin cin hanci, ake sharhi kan abin da ya jawo hakan.

Masana al'amuran da suka shafi yankin gabas ta tsakiya dai na ganin siyasar cikin gidan masarautar na daga cikin dalilan da suka sa aka kama ministocin.

Yerima Mohammed bin Salman ya ce gwamnati na fatan kwato kimanin dala biliyan $100bn daga hannun wadanda aka kama.

Lebonon: Saad Hariri ya yi amai ya lashe

Sanarwar yin murubus da kuma "dakatar da" murabus din da Firai Ministan Lebanon Saad Hariri ya yi a Saudiyya ya haifar da ce-ce ku-ce.

Mista Hariri ya ce shugaban kasa Michel Aoun ya roke shi ya dakatar da murabus din bayan Mr Hariri ya koma Lebanon a watan Nuwambar 2017.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Michel Aoun ya tattauna da Saad Hariri a fadar shugaban kasar ta Labanon

Mista Hariri ya musanta cewa Saudiyya ce ta tilasta masa yin murabus kuma ta tsare shi a kokarin dakile tasirin Iran da kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran din a Lebanon.

Bala'in girgizar kasa a Iran

Akalla mutum 330 ne suka mutu a Iran bayan wata girgizar kasa ta auka cikin wani yankin tsaunuka a kan iyakar ta da Iraki.

Hukumar bayar da agaji ta Iran ta ce mutum 70,000 na suka bukaci mafaka bayan afkuwar girgizar kasar.

Hakkin mallakar hoto REUTERS/TASNIM NEWS AGENCY
Image caption Girgizar kasar ta auku ne a lokacin da mutane da yawa ke cikin gidajensu

Girgizar data abku a wata Nuwamba tana daya daga cikin manyan girgizar kasa da suka faru a shekarar.

An kashe mutum 235 a masallacin Juma'a a Masar

Al'ummar kasar Masar za su dade suna jimamin wani harin bam da aka kai wani masallacin Juma'a da ke yankin arewacin Sinai na kasar inda ya kashe akalla mutane 235.

Wasu shaidu sun ce an kai harin ne a masallacin al-Rawda wanda ke garin Bir al-Arish yayin da ake sallar Juma'a.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An kai harin ne a wani masallaci kusa da garin al-Arish

Kasar Masar ta dade tana fama da rikice-rikice masu nasaba da 'yan gwagwarmaya a yankin Sinai tun a shekarar 2013.

'Trump ya debo ruwan dafa kansa'

Matakin da shugaba Donald Trump ya sanar cewa Amurka ta mayar da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila ya janyo kakkausar suka a fadin duniya.

Shi dai Mr Trump a lokacin da yake jawabi a fadar White House ya bayyana matakin wani abu ne da aka dade ba a yi ba a kokarin karfafa zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Hamas ta Palasdinawa ta dade tana gwagwarmaya da makamai

Sai dai kungiyar Hamas ta ce shugaba Donald Trump ya kwanto kura kuma matakin tamkar tsokanar fada ce kawai wanda babu abun da zai haifar illa fitina a yankin.

Amurka ta sha kaye kan birnin Kudus

Kusan za'a iya cewa daukacin kasashen duniya sun juyawa Amurka baya kan amincewar da ta yi wa Qudusa matsayin babban birnin Isra'ila.

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya dai ya amince da babbar murya wani kuduri da ya yi kira ga Amurka ta janye matakin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen Larabawa da na Musulmi ne suka yi kira a gudanar da taron

Kudurin ya ce duk wata shawara da ke nuna cewa Qudus ne babban birnin Isra'ila ba za ta karbu ba kuma dole a hana aiwatar da ita.

MDD ta takawa Koriya ta Arewa birki

Yayin da shekarar 2017 ke karewa ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar nuna goyon bayan sanya tsauraran takunkumi ga kasar Koriya ta Arewa.

Hakan dai wani martani ne ga gwajin wani makami mai linzami da ta yi.

Sababbin takunkuman da Amurka ta tsara daftarin su, za su yi matukar takura wa kasar ta Koriya ta Arewa game da samun man fetur da za ta shigar cikin kasar ta.

Za kuma a bukaci mayar da 'yan asalin kasar da ke aiki a kasashen waje zuwa gida wanda hakan zai katse muhimmiyar hanyar samar da kudaden kasar waje ga Koriyar ta Arewar.

Liberiya ta yi sabon shugaba shugaban kasa

Al'ummar Liberia sun zabi George Weah a matsayin sabon shugaban kasa a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a ranar 26 ga watan Disamba.

Mataimakin shugaban kasar mai ci Joseph Boakai da kuma shahararren tsohon dan wasan kwallon kafan nan George Weah su ne suka fafata a zaben.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya bayan shaharrren dan wasan kwallon kafa George Weah a lokacin gangamin yakin neman zabe

Wannan shi ne karon farko da kasar ta shirya zabe don mika mulki daga wata sabuwar gwamnati zuwa wata tun bayan yakin ba-sa-sar kasar.

Labarai masu alaka