Ba za mu rusa rundunar SARS ba — 'Yan sanda
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba za mu rusa rundunar SARS ba — 'Yan sanda

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don jin hirar da SP Almustafa Sani ya yi da BBC:

Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce babu wani abu da zai sa ta rusa rundunar nan ta musamman mai yaki da fashi da makami da ake kira SARS duk da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na soke ta.

Rundunar na mayar da martani ne ga zanga-zangar da ake yi a wasu biranen kasar ta neman a soke rundunar, bayan gangamin da aka rika yi a shafukan zumunta na neman a rushe ta bisa zargin taka hakkin bil'adama.