'Masu kunar bakin wake na shan kwaya'

Mutane sun taru a gaban motoccin da suka kone lokacin da bam ya tashi a kasuwar Monday da ke birnin Maiduguri na jihar Borno a shekarar 2014. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta kai hare hare da dama a Nigeriya

Hukumar yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi ta Majalisar dinkin duniya ta bayyanna cewa ana samun kwayar tramadol a cikin aljihun wadanda suke son kai hare-hre na kurnar bakin wake.

Hukumar ta ce yawan kwayar da aka kwace tun daga shekarar 2013 ya karu matuka daga kilo 300 zuwa tan fiye da 3 a kowce shekara.

An gano kwayoyi miliyan uku a wasu akwatuna masu tambarin Majalisar dinkin duniya a jamhuriyar Nijer a watan Satumba daya gabata.

Mayakan kungiyar Boko Haram na amfani da kwayar ta tramadol.

Kwayar da ake amfani da ita domin rage zafin ciwo, ana tsamanin cewa ana amfani da ita wajan kwantar da hankali wadanda zasu kai hari. kuma jaridar Gaurdian a baya baya nan ta wallafa rahoton da ya ce mayakan 'yan ta'ada kan zuba kwayar cikin dabino wanda suke ba yara kafin su turasu su kai hari.

Gidan tsohon shugaban Boko Haram zai zama gidan kayan tarihi

Nigeria: Sojoji sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Magumeri

An ki daukar matasa aikin asibiti saboda shan kwaya a Kano

A watan Augustan daya gabata ne aka kwace kwayar tramadol 600,000 wanda zaa kai ma kungiyar Boko Haram a kan iyakar da ke tsakanin Nigeria da Kamaru.

Wakilin UNODC a yamacin Afrika Pierre Lapaque, ya yi gargadin cewa be kamata a bar yanayin da ake ciki ya cigaba da gudana ba, saboda hakan zai yi kafar ungulu ga tsarin tsaron duniya.

"Ana ganin kwayar tramadol a cikin aljihun mutanen da aka kama, wadanda ake zargin yan ta'ada ne a yankin Sahel ko kuma wadanda suka kai harin kurnar bakin wake". a cewar Mr Lapaque

" Wannan ya sa alamar tambaya dangane da wadanda suke samar da wadannan kwayoyi ga mayakan Boko Haram da kuma al-Qaeda, ciki har da yara maza da mata wadanda suke shirin kai harin kurnar bakin wake."

Hukumar ta UNODC ta ce kwayar wadda miyagun kungiyoyi suke safarata daga Asiya da kasashen Larabawa ta koma wata babbar matsala a tsarin kiwon lafiyar yankin Sahel, musaman a arewacin Mali da Niger, inda yawan matasan da ke kasashen da ke kudu da sahara ya sa ma su safarar miyagun kwayoyi na samun kasuwa.

Wata mata a Mali ta fadawa hukumar cewa ta kan ga yara masu shekara 10 suna tafiya bayan an basu kwayar a cikin shayi domin su daina jin yunwa.

Hukumar ta UNODC ta ce mutanen da ke shan kwayar ta haramtaciyyar hanya na shan maganin fiye da kima , abin da ya zarta adadin da likitoci suke bada har sau biyar.