Yadda wani mutum ya mutu bayan ya fado daga bene hawa 62

Wu Yongning uses a selfie stick to photograph himself reclining on top of a structure far above the surrounding buildings Hakkin mallakar hoto Weibo

Wani fitaccen dan China mai kasadar hawa dogayen gine-gine ya mutu a lokacin da ya rikito daga bene mai hawa 62.

Wu Yongning ya samu dubban mabiya a shafin sada zumunta na Weibo domin kananan bidiyon da ke nuna shi kan saman dogayen gine-gine ba tare da amfani da abubuwan kare kansa ba.

Masu sha'awar bidiyonsa sun damu a cikin watan Nuwamba da suka daina ganin sakonninsa.

Yanzu haka ta bayyana cewa ya mutu bayan ya fado daga wani dogon gini mai hawa 62 a birnin Changsha.

Kafofin watsa labarai na China sun ba da rahoton cewa ya shiga wata gasa ce wadda za ta iya samar masa kyautar makudan kudi.

Dan shekara 26 din ya mutu ne ranar 8 ga watan Nuwamba, amma budurwarsa ce ta tabbatar da mutuwarsa a wani sakon da ta wallafa a shafukan sa da zumuntan China wata daya da mutuwarsa.

Abin da ake ce wa "kasancewa a saman gida" - hawa gine-gine masu tsawo sosai ba tare da kayayyakin kariya ba- yana kara samun karbuwa a duniya cikin 'yan shekaraunnan.

Sakonnin Mista Wu a shafin sa da zumunta na Weibo sun gargadi masu kallo kada su kwaikwayi irin abubuwan da yake yi. Ya samu horaswa ta fadan hannu, kuma a baya ya shiga shirye-shiryen fina-finai da na talabijin.

Amma hotunansa a saman dogayen gine-gine ne suka fi jan hankalin mutane a shafukan sa da zumunta- kuma rahotanni sun ce sun fi riba.

Hakkin mallakar hoto Weibo
Image caption Wu Yongning ya wallafa hotunan bidiyon dukkan hawan da ya yi kan shafin sa da zumuntan China Weibo

An ambaci wani dan uwansa yana cewa ya shiga wata gasa ta hawa saman bene kan kudi yuan 100,000 (daidai da fam 11,300), duk da cewa ba a bayyana nau'in gasar ba.

Jaridar South China Morning Post ta ambato wani dan uwansa yana cewa: "Ya yi shirin neman budurwarsa ta aure shi (washe garin faduwarsa)."

"Ya bukaci kudin ne domin aure, da kuma jinyar mahaifiyarsa da ke fama da rashin lafiya."

A shafin Weibo, 'yan uwa da magoya baya suna da ra'ayi mabambanta game da labarin mutuwarsa.

Labarai masu alaka