Afrika ta tsakiya: Kasar da Malamai suka gudu

Image caption Apollinaire Zaoro wani magidanci kuma manomi da ya rungumi aikin koyarwa

Iyaye sun koma koyar da 'ya'yansu a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya bayan malamai sun kauracewa makarantu saboda rikicin da ake yi a kasar.

Tun a 2013 ake rikici mai nasaba da addini da kabilanci a Afrika ta tsakiya, matakin da ya sa malamai kauracewa makarantu.

Apollinaire Zaoro, manomi ne kuma magidanci, yanzu ya sadaukar da lokacinsa domin koyar da dalibai a kauyensa da babu malamai.

Mista Zaoro ya shafe watanni uku yana bada darasi a aji mai kunshe da yara dalibai 105 a wata Makarantar da ke kauyensu kusa da Bangui babban birnin Afrika ta tsakiya.

Bangaren Ilimi ya fuskanci koma-baya shekaru da dama a Afrika ta tsakiya sannan abubuwa sun kara tabarbarewa a shekaru hudu da aka kwashe ana yaki.

Matsalolin dai sun shafi kusan dukkanin bangarorin ci gaban al'umma musamman asibitocin kananan hukumomi da wuraren shan magani.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce kusan rabin alummar kasar na dogaro ne da tallafin da kasar ke samu.

Fadan da ake gwabzawa tsakanin mayaka masu dauke da makamai ya shafi kusan kashi 80 na yankunan kasar.

Mayakan na amfani da makarantu a matsayin sansanonin yaki, inda suka mayar da tebur da kujerun dalibai a matsayin itacen abinci.

Yawancin kwararrun Malaman sun kauracewa makarantu ne saboda rashin albashi sakamakon bankuna da babu a wajen Bangui.

Barci tare da Maciji

A tsawon shekaru uku har zuwa 2016, rikicin Mayakan Seleka ya tursasawa Mista Zaoro da wasu daruruwan mazauna Yamboro kauracewa gidajensu.

Image caption Makarantu na bukatar gyra a Afrika ta tsakiya

"Muna tserewa mu shiga jeji mu buya a itace, tare da macizzai. Abincin da zamu ci ma yana gagararmu. Ko da yake mun samu sauki a lokacin da abokan adawarsu Anti-Balaka suka fatattake su. Amma har yanzu muna cike da fargaba,"

Mista Zaoro ya ce yana jin dadin aikin koyarwar, inda yake iya kokarinsa wajen koyar da yara ilimin kidaya daga 1 zuwa 100.

Yana amfani da dabarar rubuta lambobi a babbar takarda wacce ya manna a bango. Sannan zai kira lamba ya bukaci daya daga cikin daliban ya nuna a bango.

Yaran na rige-rigen nuna lambar, wanda hakan ya nuna cewa suna gane karatun da Mista Zaoro ke koyarwa.

Darasin koyon harshen Faransanci ya fi kayatarwa, inda Mista Zaoro ya kira yara biyu a gaban allo, ya umurci su yi wasan damben boxing.

Image caption Apollinaire Zaoro ya yi watsi da aikinsa na noma domin koyarwa

A 2013 ne yaki ya barke a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya bayan da mayakan Seleka musulmi suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize kirista.

Dakarun Faransa ne kuma suka kifar da gwamnatin Seleka, matakain da ya haifar da rikici tsakaninsu da Anti-Balaka.

Yanzu dakarun Majalisar Dinkin Duniya Minusca, ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui, fadar gwamnatin shugaban kasar na yanzu da aka zaba Faustin-Archange Touadera.

Image caption Dakarun Minusca ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui

Mayakan Seleka da Anti-Balaka ke rike da sauran sassan kasar, inda suke ci gaba da fada da juna domin karbe ikon hanyoyi da albarkatun kasa musamman zinari da lu'u'lu'u.

Yara Manyan gobe

Mista Zaoro na daga cikin iyaye 500 da suke koyarwa wadanda suka samu horo daga wata kungiyar agaji ta kasar Finland.

Yanzu haka akwai iyaye kimanin 8,000, da aka dauka domin ba su horo na musamman kan ilimin koyar da 'ya'yansu a makarantu.

Mista Zaoro wanda manomi ne ya ce yana alfahari da aikin ilmantar da yara wadanda sune manyan gobe a Afrika ta tsakiya. A cewarsa yana fatar ganin yaran sun samu ci gaba a rayuwa kamarsa.

Image caption Yaran da suka samu damar karatu

Zaoro da wasu sauran iyayen da ke aikin koyarwa na samun tallafin kudi dala 65 a wata daga hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ilimin yara kanana.

Amma ya ce ba suna yi ba ne saboda kudi.

"Tun da babu bankuna kuma hanyoyi ba tsaro, mun bukaci a biya mu bayan wata uku a Bangui. kuma a karshen watan Disemba ne zan fara karbar albashi" a cewar Mista Zaoro.

Rungumar aikin koyarwa da iyaye suka yi ya taimaka yara sun koma makaranta, duk da cewa tsarin bai kai nasabar tsarin ilimin kasa ba.

Yaran kauyen Yamboro ne dai ke amfana da tallafin.

A Sangala 1, wani kauye da ke nisan kilomita 70km da Bangui, duk Yanar gizo ta lullube ajujuwan, sannan da alamun albarussai da suka fasa rufin ginin makarantun.

Yara sun kauracewa makarantu saboda babu malamai, a cewar Hakimin garin Mongombe.

Hukumar UNICEF dai ta ce ba za ta iya kiyasta adadin yaran da ba su zuwa makaranta ba saboda rashin malamai.

Rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Anti-Balaka sun rungumi makamai bayan mayakan Seleka sun kifar da gwamnatin Bozize a 2013.
  • A 2013, Mayakan Seleka Musulmi suka kwace ikon gwamnati
  • Mayakan Anti-Balaka sun rungumi makamai domin yakar Seleka
  • Sama da mutane miliyan daya rikicin ya raba da gidajensu, sannan daruruwa ne aka kashe
  • Kimanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya 13,000 ke aikin wanzar da zaman lafiya da ake kira Minusca.

Labarai masu alaka