Amurkawa sun nuna wa Trump iyakarsa

Alabama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Doug Jones ya ci zaben da kashi 49.9%

Doug Jones ya zama dan jam'iyyar Democrat na farko a cikin shekaru 25 da ya ci zaben kujerar majalisar dattawa a jihar Alabama, bayan da ya tsaya takarar neman zaben tare da dan jam'iyyar Republican Roy Moore.

Nasarar Mr Jones ta bayar da mamaki kuma ta jaddada rashin amincewar Amurkawa da akidar Shugaba Donald Trump wanda ya nuna tsananin goyon bayansa ga Mr Moore ko da wasu jiga-jigan jam'iyyarsu ka ki bayar da na su goyon bayan.

Har yanzu Mr Moore bai mika wuya ba, kuma ya ce akwai sauran rina a kaba.

A lokacin gangamin neman zaben, an yi zargin Mr Moore da cin zarafin wasu 'yanmata amma ya karyata hakan.

Jihar Alabama za ta samu wakilcin Demokrat a majalisar dattawan Amurka, wanda hakan zai iya bai wa 'yan Demokrat dama wajen mamaye majalisar a zaben rabin zango a shekarar 2018.

Duk da Mr Moore bai mika wuya ba, Shugaba Trump ya yi wa Mr Jones murna a shafinsa na twitter bayan kafofin sadarwar Amurkar sun bayyana shi a matsayin wanda yayi nasarar zaben.

Labarai masu alaka