Tattaunawa kan mace-macen aure
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Tsananin soyayyar iyayen zamani ga 'ya'ya ne silar mace-macen aure'

Latsa alamar lasifikar da ke sama don jin tattaunawa kan wanann batu:

Yawan mutuwar aure a tsakanin al'ummar Hausawa ya zama tamkar ruwan dare gama duniya, al'amarin da ba haka yake ba a shekarun baya.

Duk da dai babu wata kididdiga da ke nuna yawan aurarrakin da ke mutuwa kullum, amma an yi ittifakin cewa lamarin kara muni yake.

To ko wadanne abubuwa ne suke jawo hakan a al'ummar da aka san ta da riko da addini da kyawawan al'adu?

Kan wannan batu ne Halima Umar Saleh ta tattauna da wasu iyaye mata, kuma shahararrun marubutan litattafan Hausa a arewacin Najeriya Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da kuma Hajiya Bilkisu Ahmed Funtuwa.

A hirar tasu dai, marubutan sun yi ittifakin cewa lalacewar tarbiyya a kasar Hausa, wacce ta samo asali daga dumbin soyayyar da iyayen zamani ke nunawa 'ya'yansu ce babban tarnakin da ke jawo yawan mace-macen aure.

Sun kuma kara da cewa, matsaloli kamar zurfafa soyayya don abun duniya, da samuwar kafafen sada zumunta na zamani, da kalle-kallen fina-finan ketare, da shaye-shaye miyagun kwayoyi da matsanancin kishi daga wajen mata, su ma suna taka rawa wajen jawo mace-macen aure barkatai a arewacin Najeriya.

Iyayen sun kuma ce matukar gwamnati ba ta sa hannu a lamarin ba, to fa nan da shekaru kadan al'ummar arewacin Najeriya za ta samu kanta a halin da ya fi na yanzu muni.

Labarai masu alaka