Za a fara bai wa 'yan gudun hijirar Nigeria katin shaida

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Miliyoyan 'Yan gudun hijira ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR da hukumomin Najeriya sun kaddamar da aikin bai wa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu katin shaidar dan kasa.

Ana gudanar da aikin ne a sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri babban birnin jihar Borno yankin arewa maso gabashin Najeriya

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta ce mutanen da rikcin na Boko Haram ya raba da gidajensu dubu dari daya ne zasu amfana da shirin bayar da katin shaidar a tashin farko.

Amma kawo yanzu ba a san ko zuwa karshen aikin, jimillar 'yan gudun hijira nawa ne za a bai wa katin ba.

Hukumar ta UNHCR da kuma hukumar bayar da katin zama dan kasa ta Najeriya ne ke gudanar da aikin a Maiduguri inda aka soma da sansanin 'yan gudun hijira na Dalori.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram na fuskantar matsaloli da dama a Najeriya

Hukumomin sun ce wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu da suka kai shekara goma sha shida zuwa sama ne suka cancanci a ba su katin na shaida.

Ana ganin hakan zai taimaka wajen kare su daga cin zarafi kodai daga jama'a ko daga hukumomi, tare da damar samun ilmi da harkokin kiwon lafiya ba tare da shakku ba.

Malam Ibrahin Dangana, jami'i a hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, a Maiduguri, ya shaida wa BBC cewa sun lura rashin wata shaida da ke tabbatar da mutanen 'yan gudun hijira ne kan jefa su cikin matsala.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce mutane fiye da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da suka kunshi Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

Labarai masu alaka