Bankin Duniya zai daina bayar da rancen hakar mai

Bankin Duniya zai daina bayar da rance domin aikin hakar man fetur da iskar gas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bankin Duniya zai daina bayar da rance domin aikin hakar man fetur da iskar gas

A wannan makon ne Babban bankin duniya, ya sanar da cewa zai daina samar da kudi rance don aikin hakar man fetur da iskar gas.

Babban bankin, ya sanar da hakan ne a wajen taron da ake yi kan sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa.

To sai dai kuma masana sun bayyana cewa zai yi wuya matakin da Babban bankin duniyar ya ce zai dauka ya yi wani muhimmin tasiri nan take.

Dr Ahmad Adamu, malami ne a Jami'ar Umaru Musa Yar'Adua dake Katsina, kuma masani a kan tattalin arzikin man fetur ya shaida wa BBC cewa, wannan mataki na bankin duniyar hannun ka mai sanda ne, domin ana so ne a dakile amfani da danyen mai da iskar gas.

Masanin ya ce, yawancin kasashen da suka ci gaba a duniya baki daya basu da albarkatun man fetur da iskar gas sai kasashe masu tasowa kamar Najeriya ne ke da albarkatun danyen man.

Dr Ahmad Adamu, ya ce baya ga dakile amfani da danyen man da iskar gasa, ana kuma ganin cewa danyen man fetur din da iskar gas na gurba muhalli wanda shi ke kawo dumamar yanayi.

Masanin ya ce, idan har akwai bukatar danyen man fetur da iskar gas, to duk wani yunkuri na dakile hako shi zai matukar wuya.

Dr Adamu, ya ce " Mafi yawancin hako man da ake yi kamfanoni ne na kasashen waje da kuma 'yan kasashen da ake hako man wadanda ke da hali ne ke bayar da kudin hakowa, sannan kuma bayan babban bankin na duniya da ke bayar da rancen kudin, akwai sauran bankuna da suke bayar da rancen kudi a hako man fetur din da iskar gas".

Don haka dan babban bankin shi kadai ya ce ya daina bayar da rancen kudi, to sauran kamfanoni wannan mataki ba zai yi tasiri a kan su ba inji masanin.