Dan kunar bakin wake ya kashe 'yan sanda suna fareti

A kalla jami'an 'yan sanda 13 ne suka mutu a lokacin harin
Image caption A kalla jami'an 'yan sanda 13 ne suka mutu a lokacin harin

Wani dan kunar bakin wake ya kashe a kalla jami'an 'yan sanda 13 a lokacin da suke fareti a cibiyar horar da 'yan sanda da ke Mogadishu, babban birnin Somaliya.

An kuma samu rahoton akalla wasu mutum 15 ne suka jikkata.

Dan kunar bakin waken ya yi shigar burtu ne a matsayin dan sanda, inda ya tayar da bam din a kwalejin horor da 'yan sanda ta General Kaahiye.

Kungiyar al-Shabab ta ce ita ce da alhakin kai harin. Kungiyar dai ta sha kai harin bama-bamai a birnin Mogadishu da kuma sauran biranan kasar.

Wani ganau ya ce jami'an 'yan sandan na cikin yin fareti da safe lokacin da dan kunar bakin waken ya tayar da bam din.

"Wasu daga cikin 'yan sandan sun jeru a layi, wasu kuma sun taru, a lokacin da dan kunar bakin waken da ya yi shigar 'yan sanda ya tayar da bam din," in ji Hussein Ali.

Mai magana da yawun kungiyar ta al-Shabab Abdiasis Abu Musab ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa yana kusa da gurin da aka kai harin.

A watan Oktoba ma, mayakan al-Shabab sun kai hari wani otel a babban birnin kasar inda suka kashe kimanin mutum 20.

Ko da yake kungiyar ta musanta wani harin bam da aka kai na babbar mota a birnin kasar a farkon watan Oktoba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 358.

Dakarun kungiyar tsaron Afirka kimanin 22,000 ne a kasar ke kokarin taimaka wa gwamnatin don kwato babban birnin kasar daga hannun mayakan.