Damisa ta tarwatsa taron biki

Damisa ta tarwatsa mutane suna tsaka da shagalin biki Hakkin mallakar hoto CHRISTIAN CHARISIUS
Image caption Damisa ta tarwatsa mutane suna tsaka da shagalin biki

Wasu mutane saun tsalleke rijiya da baya a wurin taron biki a Indiya, bayan da wata damisa ta yi musu dirar mikiya daga dajin da ke makwabtaka da su.

Bidiyon da abun ya faru ya nuna yadda mutane suke gudun ya- da kanin wani da kuma haura katanga don tserewa daga wurin taron.

Ba wanda ya ji rauni kuma ba dadewa damisar ta shige cikin surkukin bishiyoyi aka neme ta aka rasa.

Sai dai jim kadan kuma ta afka wa wata mata tayi mata rauni a kauyen da ke kusa da su.

Yanzu dai hukumar da ke kula da daji ta jihar Madhya Pradesh na lura da shige da ficen dabbobi, inda damisar ta taratsa yankin.

Labarai masu alaka