Kisan kiyashin Congo: 'Sai mun taka gawawwaki mu tsere'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin mutum miliyan 1.4 sun tsere daga tashin hankalin

Editan Afirka na BBC Fergal ya ziyarci yankin Kasai da ke tsakiyar JamhuriyarDimokradiyyar Congo, kasar da ake zaman makoki da manyan kaburbura.

Yau da gobe gaskiya ta gagara bayyana. Wani tarin ciyawa ne yake boye ta. Sai wasu 'yan kasuwa da kuma ragga na tufafi da ke fitowa a kasa da kuma ke jan hankali.

"Jini yana magana ," in ji "Papa" Isaac, wani tafinta jami'in Majalisar Dinkin Duniya a garin Tshimbulu da ke tsakiyar yankin Kasai.

Ya kawo mu tsakiyar wani fili inda ya ce , "jinin 'yan uwana na magana".

Babu wanda ya san iyakar gawarwakin da sojoji suka zubar a nan.

Wata mata da ke aiki kusa da mu ta matso kusa, kasancewar sojojin Majalisar Dinkin Duniya a yankin sun ja hankalinta.

Danta mai shekara 12 yana cikin wadanda aka binne a makeken kabari.

"Sojoji sun kasance suna binne gawarwaki. Mun ga inda suka tsaya da kuma yadda suka yi gina domin binne gawarwakin… wasu ba su wuce shekara 12 da haihuwa ba," in ji ta.

"Ba mayaka kawai suka kashe ba. Sun kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutuwa da kuma ciwo mai sauya halitta suna damun mutane da aka bari a baya

An fara tashin hankalin ne a bara lokacin bazara, yayin da fushin jama'a ya fito fili wanda ya haddasa bore ga gwamnatin kasar da ake yi wa kallon ta yi wa mutane nisa da kuma tafka cin hanci da rashawa, yayin da kuma ake jin tsoron jami'an tsaro.

Abu na baya da ya janyo boren shi ne kin amincewa da wani basaraken gargajiya, Kamina Nsapu, da gwmnatin ta yi tare da nada wanda take so a madadinsa.

A watan Agusta, jami'an tsaro suka kashe basaraken, amma mabiyansa sun mayar da martani, inda suka kashe duk wanda suke ganin sun hada baki da gwamnati a kashe shi.

A fadan da ya biyo baya, kusan mutum miliyan 1.4 ne suka rasa muhallinsu, kuma daga cikinsu 850,000 yara ne.

A halin yanzu garin Kasai na fama da matsalar yunwa domin manoma sun rasa muhallinsu tare da gonakkinsu.

A cikin makwanni biyu da muka yi a Kasai, barnar da aka yi ta tayar mana da hankali.

Mun ga barnar a jikin yaran da suka rame sosai da mata da yara wadanda har yanzu suna zama ne a cikin gine-ginen coci, kuma mun ji bayanai daga wadanda aka ci zarafinsu.

Mayaka sun fille kan mutane da yawa. Sojojin sun harbe mutane a kauyukan yankin.

An tube wata mata tumbur sannan aka tika ma ta kashi tare da mata fyade a bainar jama'a kafin a fille kanta domin mayakan Kamina Nsapu sun zarge ta da cin amana. An bai wa dan mijinta umarnin ya ma ta fyade.

Wani mai fafatukar rijistan zaben da za a yi a shekara mai zuwa, Prosper Ntambue, yana cikin wadanda aka ritsa da su saboda ana ganin wakilin gwamnati ne.

An kashe ofishinsa, amma ya samu ya tsira.

Duk da haka rashi ya ci gaba da addabar iyalansa: an kama 'yarsa da surukinsa, kuma aka fille musu kai.

Mene ne laifinsu? Surukinsa injiya ne wanda yake gyara wa gwamnati hanya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Miliyoyin mutane suna fuskantar barazanar yunwa bayan an tilasta wa manoma tserewa

Mista Ntambue ya nuna mini wani hoton 'ya'ya biyar na ma'auratan, da aka dauka a lokacin da suke da rai.

"'Ya'yansu sun koma marayu, saboda haka sun ci gaba da kasancewa a nan. Yanzu haka ina kula da su", kamar yadda ya shaida min.

Gwamnatin kasar ta mayar da martani ga boren da rashin tausayi. Sojoji da 'yan sanda sun mayar da hankali ga mayakan sa-kai. Yawanci mutanen kauye na amfani da makaman gargajiya tare da amfani da guru da laya da suka yi imanin cewa za su kare su daga harsasai. Amma an kashe fararen hula wadanda ba su da alaka da Kamina Nsapu.

A wasu wurare tashin hankalin ya fito da adawar da ke tsakanin kabilu, amma babban kuskure ne mutum ya bayyana abin da ya faru a matsayin wani tashin hankali mai nasaba da kabilanci

Rikici ne na talakawa da ya shafi yankunan da gwamnati ke nuna banbanci.

Mun tattauna da shedu da dama wadanda suka bayyana ta'asar jami'ar tsaro da mayakan Bana Mura da ke goyon bayan gwamnati.

Shedun da muka zanta da su sun bukaci mu boye sunayensu domin tsira da rayuwarsu daga Jami'an tsaro.

Daga gefen rafin Kasai a garin Tshikafa, wani mutum ya nuna wani wuri inda ya tuna yadda aka zube gawarwakin mutane a rafin, ruwa ya tafi da su.

"Sojoji na kwasar gawarwakin mutane su watsar a rafi. hakan ya sa mutane suka fara gudu suna buya. Amma suna bin su, su kashe sannan su watsar da gawarsu a rafi" a cewarsa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Soldiers are accused of throwing bodies off this bridge

Wata mata da ta samu mafaka a ginin wata mujami'a ta shaida muna yadda mayakan Bana Mura suka yi wa 'ya'yanta hudu yankan rago. Ta roki sojoji su shiga tsakani amma kuma ba abin da suka yi wajen hana kisan.

Wannan ya jefa rayuwarta cikin bakin-ciki, da jimamin daren kisan gillar da aka yi wa 'ya'yanta.

"Na ga mutane dauke da adda da bindigogi. Suna fille mutane, suna yanka hannu da kafafu. Dole ina ji ina gani na taka gawarwaki na tsare", a cewarta.

Wata mata ma ta shaida muna yadda mayakan suka tafi da ita tare da 'yarta 'yar shekara 15 a wata gona da ke bayan gari.

"Daga baya ne na gano an yi wa 'yata fyade", a cewarta. "Ina cike da bakin ciki a zuciyata, kan yadda aka lalata rayuwar 'yata domin yarinya ce".

A yankin Kasai, Dakarun Majalisar Dinkin Duniya ne kawai ke shiga tsakanin mutane da zaluncin jami'an tsaro da mayakan sa-kai.

Sabanin gabashin Jamhuriyyar dimokuradiyyar Congo inda dakarun na Majalisar Dinkin Duniya ba su aiki tare da sojoji a Kasai.

Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar matsin lamba. tana da yawan Sojoji kasa da 20,000 a fadin Congo, kasar da girmanta ya kai kashi biyu bisa uku na fadin yammacin Turai.

Kuma duk da haka an datse yawan dakaru 3,000 bayan da Amurka ta rage yawan kudaden tallafin da ta ke bayar wa ga aikin wanzar da zaman lafiya a Majalisar Dinkin Duniya.

Duk wanda ya ziyarci Kasai a kwanan nan, zai tabbatar da cewa babu wani kwanciyar hankali a yankin.