Mallika Sherawat ta ‘kasa’ biyan kudin hayar gida a Paris

Bollywood star Mallika Sherawat

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Malika Sherawat 'yar fim da ta kasa biyan kudin haya a Paris

Fitacciyar 'yar fim din Bollywwod Malika Sherawat na fuskantar barazanar kora daga gidan da ta take haya tare da mijinta a Paris.

Ana bin Ma'auratan bashin kudin haya da suka kai 80,000 na yuro, kuma an tsayar da ranar da kotu za ta yanke hukunci game da batun a Paris.

Lauyan da ke kare ma'auratan ya ce da gangan suka ki biyan kudin hayar saboda harin da aka kai wa 'yar fim din a cikin gidan a bara.

Amma yanzu haka wanda ke da mallakin gidan ya bukaci a kwace kayayyakin da suka mallaka a cikin gidan hadi da agogo mai tsada.

Gidan da Malika Sherawat ke haya yana cikin gidajen unguwar masu hannu da shuni da ake kira "16 Arrondissment" a Paris inda mafi yawanci ofisoshin jekadan kasashen waje suke.

Lauyan da ke kare mai Mai gidan ya ce babu wata tattaunawar da suke tsakaninsu game da sabunta hayar, duk da cewa Malika da mijinta suna da halin biyan hayar.

Ko da yake lauyan ma'aurantan ya amsa cewa suna cikin yanayi na rashin kudi.

Malika Sherawat ta fito a finafinan Bollywood sama da 40.