Sojin Nigeria sun fatattaki 'yan Boko Haram a Minok

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram na ci gaba da zama barazana a Najeriya

An kashe 'yan Boko Haram 14 a wata musayar wuta da suka yi da sojojin Najeriya, a yayin da mayakan suka yi kokarin kwace wani sansani a jihar Borno.

Kamfanin dillacin labaran AFP ya ce mayakan na Boko Haram sun abka sansanin sojin cikin manyan motoci takwas a ranar laraba, amma sojoji sun yi nasarar fatattakarsu a sansaninsu da ke kauyen Mainok a jihar Borno.

Musayar wutar ta tilastawa matafiya tsakanin Maiduguri zuwa Damaturu fakewa a kauyen Jakana na tsawon lokaci.

Amma rahotanni sun ce an sace wasu motocin yaki na sojin Najeriya bayan arangamar da suka yi mayakan na Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya da ke fada Boko Haram a Borno ta tabbatar da harin tare da cewa dakarunta sun murkushe maharan.

A watan Satumban 2013 mayakan Boko Haram sun taba rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a daidai Benisheik da ke kusa da Minok inda suka kashe mutane 167.

Mafi yawanci dai mayakan Boko Haram na kai hare-hare ne da motocin sojin Najeriya da suka sace.

Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk da ana ikirarin an karya lagonsu.