Gwamnonin Nigeria sun amince a kashe $1bn don yaki da Boko Haram

Nigeria Boko Haram Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Gwamnonin Jihohi 36 sun tattauna matsalar tsaro da karancin Fetur

Gwamnonin jihohin Najeriya sun goyi bayan a kashe kudi dala biliyan daya domin yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari shugaban gwamnonin jihohin kasar 36 ne ya sanar da matakin a taron majalisar zartarwa da aka gudanar, wanda Farfesa Yemi Osibanjo ya jagoranta a fadar shugaban kasa a Abuja.

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya shaidawa manema labarai cewa gwamnonin sun amince gwamnatin Tarayya ta kashe kudi dala biliyan daya domin yakar Boko Haram.

Za a dai kashe kudaden ne daga asusun rarar kudin mai na kasar.

Gwamnonin sun ce sun amince a kashe kudaden ne saboda ci gaban da aka samu a yaki da Boko Haram.

Boko Haram dai na ci gaba da zama barazana a arewa maso gabashin kasar, inda mayakan kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake tare da kashe fararen hula.

Gwamnonin kuma sun tattauna matsalar karancin fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya, inda karamin ministan albarkatun mai ya yi alkawalin cewa za a kawo karshen matsalar nan da sa'o'i 48.

Har yanzu ana fama da dogayen layi a gidajen mai a manyan biranen Najeriya, kasar da ta fi arzikin mai a nahiyar Afirka.