Da gaske Facebook na raba kan jama'a?

Chamath Palihapitiya ya yi aiki a Facebook lokacin da kamfanin ke bunkasa sosai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chamath Palihapitiya ya yi aiki a Facebook lokacin da kamfanin ke bunkasa sosai

Facebook ta mayar da martani ga wani tsohon ma'aikacinta wanda ya ce shafin sada zumuntar da makamantansa na raba kan jama'a.

Chamath Palihapitiya ya yi bayanin ne a watan jiya amma a ranar Litinin ne aka yada labarin a shafukan intanet.

Facebook ya fitar da wata sanarwa domin kare kansa.

Wani mai magana da bakin kamfanin ya ce Mr Palihapitiya bai wuce shekara shida ba ya na aiki da Facebook.

"Lokacin da Chamath ya ke aiki a Facebook, mun mayar da hankali wajen kirkiro sabbin hanyoyin inganta shafukan sada zumunta da kuma bunkasa Facebook a fadin duniya. Facebook ya bambamta da sauran kamfanoni a lokacin kuma da muka kara bunkasa sai muka gane cewa nauyin da ke kanmu shi maya karu."

Mr Palihapitiya, wanda a da shi ne mataimakin shugaban Facebook ne na fannin bunkasa masu amfani da shafin, yanzu wani fitaccen dan kasuwa ne.

Shi ne sabon jami'in wata kungiya wacce ta ke nuna damuwarta game da illar al'adar tambarin "Like"- wani yanayi mai nuna cewa jama'a da dama sun dogara ga shafukan sada zumunta wajen samun nutsuwa da farin ciki.

"Mun kirkiro abubuwan da ke wargaza ginshikin yadda zamantakewa ta ke," in ji Mr Palihapitiya.

Ba shi kadai ke da wannan ra'ayi ba. Sean Parker, Shugaban Facebook na farko kuma wanda ya tsara da yawa daga cikin shirye-shiryen kasuwancin kamfanin, ya nuna nadamarsa dangane da rawar da ya taka a tarihin Facebook.

“Allah kadai ya san abunda Facebook ke yi wa kwakwalwar yaranmu," ya gaya wa Mike Allen daga shafin labarai na Axios.

"Mu na daukar aikinmu da muhimmanci kuma mu na iya kokarinmu wajen ganin mun ci gaba," sanarwar ta Facebook ta ci gaba da cewa.

"Mun yi aiki gami da bincike mai yawa tare da wasu masana daga waje da kuma malamai domin fahimtar irin tasirin da ayyukanmu ke yi a kan lafiya, sannan mu na amfani da shi wajen ci gaban kamfaninmu."

"Kuma mu na samun masu zuba hannun jari da kuma kimiyya- kamar yadda Mark Zuckerber ya ce a taronmu na karshe, mu na fatan mu rage ribarmu domin ganin mun zuba hannun jari a inda ya kamata."

Duk da wadannan manyan jami'an kamfanonin sun bayyana ra'ayoyinsu, fannin kasuwancin kamfanin Facebook din ya jajirce wajen isar da nufin kamfanin.

A makon jiya ne su ka fitar da sabon shafinsu na yara, wanda shi ne shafinsu na farko domin yara 'yan kasa da shekara 13.

Labarai masu alaka