An dakatar da zirga zirgar jiragen sama a sabon filin saukar jiragen sama na Dakar babban birnin Senegal

Na'urar kulla da tashi da saukar jiragen sama
Image caption Na'urar kulla da tashi da saukar jiragen sama

An dakatar da tashi da saukar jiragen sama a sabon filin jirgin sama na Dakar babban birnin kasar Senegal.

Ma'aikatan filin jirgin saman dai sun shiga yajin aiki ne mako guda bayan da aka bude filin jirgin saman.

Ma'aikatan na korafi kan batun albashi da sauran hakkokin su lamarin daya haifar da tsaiko a zirga zirgar jiragen sama a baki daya.

Daruruwan matafiya ne lamarin ya rutsa da su sakamakon yajin aikin.

Paul Francois Gomis shugaban kungiyar kwadon ya shaidawa BBC cewa ''masu kula da harkar zirga-zirgar jiragen sun nuna rashin gamsuwar da yadda yanayin aikin ke gudana.

Kamfanonin jiragen kasar Portuguese ko kuma Portugal sun sanar da cewa an dage tashi da kuma saukar wasu jiragen su.

A halin yanzu kamfanonin jirage da dama na karkata akalar su zuwa Banjul babban birnin Gambia.

Shi dai wannan sabon filin saukar jirage na Blaise Diagne an kashe dala miliyan 600 wajen gina shi.

Yajin aikin dai zai kasance na kwana guda ne to sai dai duk da haka matafiya da dama sun shiga wani mawuyacin hali .

Labarai masu alaka