Nigeria: An 'hana' Musulma zama lauya saboda ta sanya hijabi

A halin yanzu dai Firdaua ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta "kira ta"
Image caption A halin yanzu dai Firdaus ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta "kira ta"

An hana wata 'yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama lauya - mai iya aiki a kotu - saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.

Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.

Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet na Nigerianlawyer.com.

Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A jihar Legas ma dai sai da aka kai maganar saka hijabi a makarantin sakandare kotu

Wata mata dai ta wallafa wani sako a shafin sa da zumunta na Instagram inda ta yi korafin cewa masu kula da lamuran dokar Najeria sun yi wa wata "'yar uwa" wariya tana mai amfani da maudu'in #justiceforFirdaus.

Tuni dai 'yan Najeriya suka yi ta tafka muhawara a kotu kan hana mai saka hijabin zama lauya.

Wannan batu dai shi ne ya mamaye kafofin sada zumunta a Nigeria tun daga ranar da wannan abun ya faru.

Misali wasu ma'abota shafukan twitter sun yi ta yada hotunan ita wannan daliba da aka hanata zama cikakkiyar lauya.

Wasu kuma sun yi ta yada hotunan daya daga cikin 'ya'yan shugaban Najeriya wacce a bara ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin lauya.

Shima shugaban Kungiyar lauyoyin wato A B Mahmoud ya wallafa wani hoto na 'yarsa a shafinsa na twitter inda a hoton ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin lauya a birnin New York na kasar Amurka.

Ya kara da cewa kungiyar lauyoyi ta Najeriya za ta yi kokarin ganin an kawo karshen wannan batu na hana lauyoyi masu son sanya hijabi.

Labarai masu alaka