'Madrid na zawarcin Mohamed Salah'

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Gasar Firimiya na watan Nuwamba

Kocin tawagar Masar Hector Cuper ya ce kungiyar Real Madrid tana zawarcin dan wasan Liverpool Mohamed Salah, yayin da Kocin Madrid Zinedine Zidane ya ce yana jinjina wa kwarewar dan kwallon, kamar yadda jaridar Daily Sun ta bayyana.

Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar BBC na Afirka na bana a farkon makon nan.

Tsohon Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti zai koma Chelsea a matsayin sabon kocinta a kakar wasa ta badi, a cewar jaridar Daily Record.

Dan wasan Chelsea Batshuayi zai bar kungiyar a watan gobe amma zai tafi aro ne, kamar yadda jaridar London Evening Standard ta bayyana.

Kocin Manchester United Jose Mourinho zai sayi sabbin 'yan wasa a watan gobe duk da cewa shi ba mai kaunar yin hakan ba ne a kasuwar saye da 'yan wasa ta watan Janairu, in ji jaridar Daily Mail.

Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona ya ce ya ba Madrid shawarar ta sayi Kylian Mbappe gabanin kungiyar PSG ta riga ta, in ji kafar yada labarai ta Goal.com

Jaridar Liverpol Echo ta ce kungiyoyin Brighton da Aston Villa suna neman dan wasan Liverpool Marko Grujic a matsayin aro a watan Janairu.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta tattauna da Jack Wilshere a karshen watan nan don sabunta zamansa a kungiyar, a cewar jaridar London Evening Standard.

Tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ya aske sumar da ke kansa, wadda ya kwashe shekara 17 yana tara ta, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twiter shafe.

Hakkin mallakar hoto Twitter/Didier Drogba
Image caption Didier Drogba bayan ya yi sabon aski

Labarai masu alaka