Man City ta yi wa Tottenham ruwan kwallaye

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gündogan ne ya fara zura kwallo a raga Tottenham a minti na 14

Manchester City ta lallasa Tottenham a wasan da suka yi gumurzu ranar Asabar inda suka tashi wasan 4-1.

Hakan yana nufin kungiyar ce za ta ci gaba da jan ragama a teburin gasar, inda take maki 52.

Sakamakon ya sa Tottenham ta koma matsayi na bakwai a teburin Gasar Firimiya da maki 31.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar a ranar Asabar su ne:

  • Leicester 0-3 Crystal Palace
  • Arsenal 1-0 Newcastle
  • Brighton0-0 Burnley
  • Chelsea 1-0 Southampton
  • Watford1-4 Huddersfield
  • Stoke 0- 3 West Ham

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka