Man Utd ta doke West Brom

Man Utd Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta doke West Brom a wasan da suka yi gumurzu ranar Lahadi inda suka tashi wasan 2-1.

Romelu Lukaku ne ya zura kwallon farko a ragar West Brom a minti 27 na da fara wasan.

Daga nan ne sai Jesse Lingard ya kara jefa kwallo ta biyu a minti na 35 na fafatawar.

Bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ne Gareth Barry ya farke wa kungiyarsa kwallo daya a minti na 77 na gumurzun, inda aka tashi wasan 2-1.

Har yanzu United tana ta biyu a teburin firimiya da maki 41, yayin da suke da tazarar maki 11 tsakaninsu da ta daya a teburin Manchester City inda take da maki 51.

Ita kuwa West Brom tana ta 19 a teburin firimiya da maki 11.

Hakazalika kungiyar Liverpool ta lallasa Bournemouth da ci 4-0.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka