'Za mu magance matsalar shan miyagun kwayoyi a Nigeria'

Shugaban Majalisar dattawan Nigeria Sanata Bukola Saraki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanata Bukola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki za su lalubo hanyoyin magance matsalar shan miyagun kwayoyi

Majalisar dattawan Najeriya ta shirya taro na kwana biyu a birnin Kano don tattauna yadda za a magance matsalar shan miyagun kwayoyi da ke addabar al`umma.

Majalisar ta ce ta shirya taron ne da za'a fara ranar Litini bayan ta kadu da wasu alkaluma da ke nuna cewa matsalar ta yi kamari musamman a arewacin kasar.

Wasu rahotonni sun nuna cewa a kowace rana akan sha a kalla kwalbar kodin miliyon uku a jihohin Kano da Jigawa kadai.

Shugaban ma`aikata a ofishin shugaban majalisar dattawa Dr Hakkim Baba Ahmed ya ce sun gayyato masana da sauran masu ruwa da tsaki don lalubo hanyoyin magance matsalar shan miyagun kwayoyi da ke addabar al`umma.

A baya dai matasa ne aka sani da wannan dabi'u na ta'ammali da kayen maye.

Sai dai yanzu lamarin ya zama tamkar ruwan dare a tsakanin mata da 'yanmata a arewacin Nijeriya.

Babban kalubalen da ake fuskanta a yaki da wannna dabi'a shi ne yadda masu shan kayan mayen ke samun kayan hadin cikin sauki.

Masana dai sun ce idan ba a gagguta daukar matakin dakile wannan dabi`a ba, to a karshe za a samar da wata al`uma marar kan-gado.

Labarai masu alaka