An zabi sabon shugaban kasa a Chile

Wannan shi ne karo ba biyu da Mr Sebastián Piñera ya zama shugaban kasar Chile Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan shi ne karo ba biyu da Mr Sebastián Piñera ya zama shugaban kasar Chile

Attajirin nan dan jam'iyyar conservative Sebastian Pinera ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Chile.

Mr Pinera, wanda tsohon shugaban kasar ne ya samu kashi 55 cikin 100 yayin da abokin takarar sa Alejandro Guillier na jam'iyyar masu ra'ayin kawo sauyi ya samu kashi 45.

Mr Pinera ya yi alkawari rage yawan haraji don farfado da tattalin arzikin kasar.

Wannan dai shi ne karon farko tun bayan komawar kasar tafarkin demukradiyya da ba'a samu mutane sosai sun fito zabe ba.

Kasa da rabin al'ummar kasar masu katin zabe ne kawai suka fito don kada kuri'a.

Masu sharhi sun ce 'yan kasar da dama sun yanke kauna game da shugabancin kasar bayan badakalar cin hanci tsakanin 'yan siyasa da aka yi ta bankadowa.

Labarai masu alaka