Rashin wuta ya sa dubban fasinjoji sun makale a filin jirgin Amurka

Passengers at Hartsfield-Jackson airport Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hartsfield-Jackson shi ne jirgin sama mafi hada-hada a duniya

Wutar lantarkin da aka dauke a filin jirgin saman Hartsfield-Jackson da ke birnin Atlanta na kasar Amurka ranar Lahadi ya jefa dubban fasinjoji cikin dimuwa da rashin sanin inda za su sa kansu.

Filin jirgin shi ne wanda aka fi hada-hada a cikinsa a duniya, inda a kullum fasojoji 250,000 ke ratsawa ta cikinsa yayin da jirgi 2,500 ke sauka.

An bar fasinjoji cikin duhu a farfajiyar filin jirgin da kuma wadanda suka hau jirage amma ba su iya tashi ba.

An dawo da wutar ta lanatarki a filin jirgin, ko da yake sai da aka soke tashin jirage sama da 1,000 ranar Lahadi kuma ana sa rai za a soke tashin wasu ranar Litinin.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An soke tashin jirage da dama

Kamfanonin jiragen sama da dama, cikinsu United, Southwest da kuma American Airlines, sun soke tashin jiragensu ranar Lahadi.

IHotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna fasinjoji a zaune cikin duhu. Wasu kuma sun ba da labarin zama a cikin jirgi ba tare da ya tashi ba tsawon awa shida.

Wata fasinja, Jannifer Lee na cikinsu inda za ta je birnin Minnesota daga Florida tare da kyanwarta 'yar shekara goma.

Andakatar da jirgin da take ciki tsawon awa hudu.

Hakkin mallakar hoto Jannifer Lee
Image caption Ms Lee ata kyanwarta sun shafe awa hudu suna makale

"Na so yin sa'ar tafiya cikin sauki musamman da yake ina tare da kyanwata", ta shaida wa BBC.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin saman Dubai na cikin jiragen da suka soke tashi

Labarai masu alaka