A shirye nake na yi gwajin miyagun kwayoyi — Sarki Sanusi

Sarki Sanusi ya bukaci Shugaba Buhari ya dauki matakin gaggawa Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Sarki Sanusi ya bukaci Shugaba Buhari ya dauki matakin gaggawa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce a shiye yake a yi masa gwajin miyagun kwayoyi a yunkurin da yake yi na ganin an magance matsalar a jihar.

Sarkin ya bayyana haka ne ranar Litinin a wurin taron kwana biyu da Majalisar dattawan Najeriya ta shirya a birnin Kano kan yadda za a magance matsalar shan miyagun kwayoyi da ke addabar al`umma.

A cewarsa, matsalar shan miyagun kwayoyi ta shafi kusan dukkan iyali a arewacin Najeriya.

"Gaskiyar lamari shi ne yawancin 'ya'yan masu hali da ke tu'ammali da miyagun kwayoyi sun tashi ne sun gani a gidajensu", in ji Sarkin na Kano.

Mai martaba Sarki Sanusi II ya yi kira ga mahukunta su dauki matakin gaggawa domin shawo kan matsalar.

Ya kara da cewa rashin aiwatar da dokokin da aka yi ne ya sa matsalar ke ta'azzara.

Sarki Sanusi ya soki 'yan siyasar kasar, wadanda ya ce suna bai wa matasa kayan maye domin su kare bukatunsu.

Ga wasu kalaman da Sarki Sanusi II ya yi:

A farkon watan nan ma, sai da Sarki Sanusi ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki matakin magance wannan matsala a lokacin da ya kai ziyara Kano.

Ya ambato wasu alkaluma da ke nuna cewa ana shan miyagun kwayoyi dangin kodin sama da kwalba miliyan uku a kowacce rana a jihar ta Kano da Jigawa.

A baya dai matasa ne aka sani da wannan dabi'u na ta'ammali da kayen maye.

Sai dai yanzu lamarin ya zama tamkar ruwan dare a tsakanin mata da 'yan mata a arewacin Najeriya.

Babban kalubalen da ake fuskanta a yaki da wannna dabi'a shi ne yadda masu shan kayan mayen ke samun kayan hadin cikin sauki.

Masana dai sun ce idan ba a gagguta daukar matakin dakile wannan dabi`a ba, to a karshe za a samar da wata al`uma marar kan-gado.

Labarai masu alaka