Buhari ya kara wa shugabannin soji wa'adin shugabancinsu

Har yanzu akwai jan aiki a gaban manyan hafsan sojin Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Har yanzu akwai jan aiki a gaban manyan hafsan sojin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin shugabancin manyan hafsan hafsoshin sojin kasar.

Manyan hafsan sojin su ne Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, hafsan hafsoshin tsaron Najeriya; Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, hafsan dakarun sojin kasa; Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, hafsan dakarun sojin ruwa da kuma Air Marshal Baba Sadique Abubakar, babban hafsan sojin sama..

Wata sanarwa da ta fito daga ministan tsaro Mansur Muhammad Dan-Ali ta ce an kara wa sojojin wa'adi ne bisa la'akari da jajircewarsu wajen kawar da Boko Haram da kawo zaman lafiya a yankin Naija Delta.

"An tsawaita wa'adin nasu ne bisa ikon da sashe na 218 (1) da (2) na kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa shugaban kasa.

An nada manyan hafsan sojin ne a watan Yuli na shekarar 2015 a lokacin da rikicin Boko Haram ke nema ya gagari kundila.

Masu sharhi kan sha'anin tsaro sun ce ko da yake manyan hafsan sojin suna bakin kokarinsu a yunkurin magance matsalolin tabarbarewar tsaro, amma har yanzu akwai gagarumin aiki a gabansu musamman saboda yadda 'yan kunar bakin wake ke ci gaba da tayar da bama-bamai a arewa maso gabashin kasar.

Labarai masu alaka