Cyril Ramaphosa ya zama sabon shugaban jam'iyyar ANC

Cyril Ramaphosa gestures at an election rally of the ruling African National Congress (ANC) in Port Elizabeth, South Africa (April 16, 2016) Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cyril Ramaphosa ya yi alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa

Jam'iyyar da ke mulkin Afrka ta Kudu African National Congress (ANC) ta zabi Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugabanta domin maye gurbin Shugaban Jacob Zuma.

Mataimakin shugaban kasar ya kayar da tsohuwar matar Zuma, Nkosazana Dlamini-Zuma bayan an yi fafatawa mai zafi.

Mr Ramaphosa yana da gagarumin kwarin gwaiwar zama shugaban kasar a shekarar 2019.

Neman shugabancin jam'iyyar ya haddasa baraka a cikin jam'iyyar inda aka rika yin fargaba za ta iya darewa kafin zaben da ke tafe.

Mr Ramaphosa ya samu kuri'a 2,440 yayin da Ms Dlamini-Zuma ta samu kuri'a 2,261, in ji wata sanarwa da kakakin jam'iyyar ANC ya fitar.

Fitar da sakamakon zaben ya sanya wakilan jam'iyyar sun barke da shewa da murna a birnin Johannesburg da kan tituna.

Wasu rahotanni da aka soma bayarwa sun ce an dakatar da fitar da sakamakon zaben da fari, inda masu goyon bayan Ms Dlamini-Zuma suka bukaci a sake kidaya kudi'un.

Mr Ramaphosa, mai shekara 65, ya yi alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa da ke faruwa a cikin gwamnati kuma 'yan kasuwa na goyon bayansa.

Ms Dlamini-Zuma, mai shekara 68, ta rika sukar irin ikon da 'yan kasuwa farar fata ke da shi sanna ta sha alwashin kawar da abin da ta kira wariyar launin fara.

Labarai masu alaka

Karin bayani