An nada Thierry Henry sarautar 'Igwe' a Nigeria

Tsohon dan kwallon Arsenal da Faransa Thierry Henry Hakkin mallakar hoto Femi Coker
Image caption Igwe Thierry Henry

An nada tsohon dan kwallon Arsenal da Faransa Thierry Henry sarautar Igwe da magoya bayansa suka dade suna kiransa a Najeriya.

An nada Henry a matsayin "Igwe", wato basarake a harshen kabilar Igbo, sarauta da masu goyan bayansa a kudu maso gabashin Najeriya suka nada masa.

Hakkin mallakar hoto Twitter Femi Coker
Image caption Henry ya yi shigar gargajiya irin ta 'yan kabilar Igbo

Ya yi shigar gargajiya irin ta 'yan kabilar Igbo, inda ya sa jar hula, ya rike mafici, da kuma hadimai a kusa da shi, ko da yake ba a hukumance aka yi nadin sarautar ba. An yi bikin nadin ne a wani wajen bikin da kamfanin Guinness ya shirya.

Hakkin mallakar hoto Twitter Femi Coker
Image caption An dade ana kiran Henry da sunan Igwe a Najeriya

A ranar Lahadi ne Henry ya je Lagos domin ganawa da mutanen da suka yi nasara a gasar da kamfanin Guinness ya shirya, inda aka dauki hoton shi yana taya masu dafa abinci a wurin taron.

Labarai masu alaka