Ana zargin Yariman Saudiyya da sayen gida mafi tsada a duniya

Gidan alfarman da ake zargin yarima mai jiran gado na Saudia ya siya a Faransa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hoton gidan alfarmar da ake zargin yarima mai jiran gado na Saudiyya ya siya a Faransa

Jaridar New York Times ta Amurka, ta rawaito cewa yarima mai jiran gado a Saudiyya, Mohammed Bin Salman, shi ne ya sayi wani gida na alfarma a boye a kasar Faransa.

Jaridar ta ce, takardun cinikin gidan da aka yi a shekarar 2015, an gano cewa shi ya sayi gidan ta hanyar amfani da wasu dumbin kamfanoni da aka yi wa rijista.

Gidan wanda ke dab da fadar shugaban kasar Faransa, yana da wurin ajiyar giya na karkashin kasa da sinima da korama da kifaye masu alfarma nau'in koi, da sturgeon da kuma wurin shakatawa na alfarma da ke karkashin kasa.

Kudin gidan dai ya kai dala miliyan 320, wanda mujallar Fortune ta kira shi da gidan da ya fi sauran gidaje tsada a duniya.

To sai dai kuma gwamnatin Saudiyya ba ta ce komai ba a kan rahoton.

Mai magana da yawun ofishin jakadancin Saudiyya a Amurka, ta zargi ma'aikatan jaridar da yin rahoto son rai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yarima Muhammad bin Salman na Saudia, na yaki da cin hanci da rashawa a kasar

A watannin baya-bayan nan, Yarima Mohammed, ya jagoranci yaki da cin hanci da rashawa da cin amanar kasa da kuma yadda ake nuna wa wasu gata a kasarsa.

A shekarar 2015, an rawaito cewa, yariman ya sayi wani jirgin ruwa na alfarma daga wajen wani hamshakin dan kasuwa a Rasha a kan kudi dala miliyan 590.

Kazalika jaridar ta New York Times, ta rawaito cewa shi ne kuma ya sayi wani zane na Salvator Mundi, wanda Leonardo da Vinci ya yi a kan kudi dala miliyan 450.

Labarai masu alaka