'Ba a kashe ma'aikatan shirin samar da abinci na duniya ba'

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY
Image caption Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, mutane hudun da aka kashe yayin harin da wasu 'yan bindigar da ake zaton mayakan Boko Haram ne su ka kai kan ayarin motocin shirin samar da abinci na duniya, ba ma'aikatan shirin ba ne.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Birgediya Janar Sani Usman KukaSheka, ya shaida wa BBC cewa, ko shakka ba bu an kai wa sojojin hari a lokacin da suke fitowa daga kauyen Dikwa zasu nufu Ngala, a loakcin ne 'yan Boko Haram din suka musu kwantan bauna, amma nan take suma suka mayar musu da martani inda har suka kashe 'yan Boko Haram shida.

Birgediya Janar Sani Usman KukaSheka, ya ce suma 'yan Boko Haram su kashe mutum hudu wadanda rundunar sojin ke tafiya tare da su amma ba ma'aikatan shirin samar da abinci na duniya ba ne.

A ranar Asabar din da ta gabata ne, wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, suka kai hari kan yarin motocin shirin samar da abinci na duniya inda suka kashe mutum hudu.

Mayakan sun yi wa ayarin motocin da sojoji ke yi wa rakiya kwanton bauna ne.

Shaidu sun ce maharan sun zo ne cikin wa su motoci biyu inda suka budewa ayarin motocin wuta kuma suka sace abinci a daya daga cikin motocin jami'an agajin.

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram, tana mai cewa ba su da katabus din kai manyan hare-hare.

Sai dai 'yan kungiyar na ci gaba da kai hare-hare na kunar bakin wake a arewa maso gabashin kasar.

Ya zuwa yanzu mayakan Boko Haram sun kashe fiye da mutum 20,000 a shekaru takwas da suka shafe suna kai hare hare a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.

Labarai masu alaka