'Sai iyaye da al'umma sun hada kai za a yaki shaye-shaye'

Matsalar shaye-shaye ta addabi Najeriya musaman arewacin kasar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matsalar shaye-shaye ta addabi Najeriya musaman arewacin kasar

Wasu masu ruwa da tsaki a harkar yaki da shaye-shaye a Najeriya sun ce babu wani matakin da zai magance matsalar, har sai iyaye da al'umma baki daya sun hada kai wajen yakarta.

Sun bayyana ra'ayin nasu ne a wajen wani taro da majalisar dattawan kasar ta shirya a birnin Kano don samar da mafita.

Baba Umar Galadima, shi ne mataimakin shugaban kungiyar fadakar da matasa a kan illolin shaye-shaye da aka fi sani da Youth Awareness Forum on Drug Abuse, a Kano.

Ya kuma shaida wa Ibrahim Isa na BBC cewa shi ma ya yarda da wannan ra'ayin.

Sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron yadda hirar tasu ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jawabin Baba Umar Galadima kan shaye-shaye