Super Eagles da 'yar Nigeria na takarar cin kyautar CAF

Mohamed Salah da P.Emerrick Aubamenyang da kuma Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Twitter/@CAF_Online
Image caption Mohamed Salah da P.Emerrick Aubamenyang da kuma Sadio Mane

An bayyana 'yar kwallon Najeriya, Asisat Oshaola a cikin 'yan takarar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta Afirka ta shekarar 2017.

Wata sanarwar da hukumar kwallon ta Afirka ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce Chrestina Kgatlana ta Afirka ta Kudu da Gabrielle Onguene ta Kamaru su ne sauran masu takarar cin kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta wannan shekarar.

A fagen maza kuwa Mohamed Salah da ya ci kayutar gwarzon kwallon kafar Afirka ta BBC a shekarar 2017 yana cikin 'yan wasan kwallon kafa uku masu takarar cin kyautar.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@CAF_Online
Image caption Asisat Oshoala da Chrestina Kgatlana da kuma Gabrielle Oguene

Sauran wadanda suke takarar cin kyautar gwarzon kwallon kafa ta Afirkan sun hada da Pierre Emerrick Aubameyang da kuma Sadio Mane.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@CAF_Online
Image caption Indomitable Lions ta Kamaru da Pharaohs ta Masar da kuma Super Eagles ta Najeriya

Cikin masu horars da 'yan wasa kuwa kocin Super Eagles Gernot Rohr da kocin Pharoahs na Masar, Hector Cuper da kuma L'Hussein Ammouta na kungiyar kwallon kafa ta Wydad Casambalanca su suke takarar zama kocin da ya fi ko wanne a nahiyar Afirka.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@CAF_ONLINE
Image caption Gernot Rohr na Super Eagles da Hector Cuper na Pharoahs da kuma L'Hussein Ammouta na Wydad Casablanca

A fagen tawagogin kwallon kafan maza ta kasashen nahiyar kuwa Supera Eagles din Najeriya da Indomitable Lions ta Kamaru da kuma Pharaohs ta Masar ne ke takarar zama tawagar da ta fi ko wace iya taka leda a nahiyar cikin shekarar 2017.

Cikin tawagogin kwallon kafa na mata a kasashen Afirka kuwa Falconets ta Najeriya da Black Princesses ta Ghana da kuma Bayana-Bayana ta kasar Afirka ta Kudu su suke takarar zama tawagar da ta fi ko wacce a nahiyar Afirka a shekarar 2017.