Kun san gidan yarin da fursunoni ke iyo cikin fitsari?

Gidan yarin Liverpool Hakkin mallakar hoto HMIP
Image caption Masu sa ido a gidan yarin na Liverpool sun ga yadda ake rayuwa cikin kazanta kamar ban-dakin da ba a iya wanke wa

Fursunoni a gidan yarin Liverpool na rayuwa a yanayi mafi muni da wata tawagar masu sa ido ba su taba gani ba a duniya, a cewar wani rahoto da BBC ta gani.

Beraye da kyankyasai ne cike a gidan yarin, kamar yadda wani bangare ke cike da kazanta da ba a iya tsabtacewa.

Takardun binciken da aka bankado sun ce wasu fursunonin na rayuwa a kurkukun da ya kamata a ce ma an daina amfani da shi, saboda lalacewarsa musamman ban-daki.

Ma'aikatar shari'a ba ta ce komi ba a kan bayanan ba da aka bankado.

Tawagar masu sa ido a gidajen yari sun kai ziyarar ba-zata ne a gidan yarin na Liverpool a watan Satumba bayan sun samu labarin halin da ya ke ciki.

Abubuwan da suka gano, a cewar rahoton, babbar matsala ce ga samar da tsabtataccen muhalli.

Hakkin mallakar hoto HMIP
Image caption Babu wani tsari da aka yi tanadi na kawo karshen matsalar Beraye da kyankyasai a cewar rahoton

Tawagar kwararrun sun ce ba za su taba iya tuna wani gidan yari mafi muni kamar na Liverpool ba.

A lokacin da yake ba da labarin abin da ya gani a gidan yarin, babban sufeton gidajen yari Peter Clarke, ya kasa boye bacin ransa.

"Na sami wani fursuna da ke cikin wani hali na rashin lafiya kuma yake matukar bukatar kulawa wanda ake tsare da shi a wani dakin da babu ko kujera balle gado," a cewarsa.

"Tagogi da kayan ban-dakin da ake tsare da shi duka sun karye, sannan ban-dakin kamar ya cika ko kuma ya toshe, yana diga kuma yana rayuwa ne a duhu".

"Musamman ma wannan mutumin ana tsare da shi a cikin wannan yanayin a tsawon makwanni."

Hakkin mallakar hoto HMIP
Image caption Masu sa ido sun ga yadda tagogi suka lalace a gidan yarin

Babban abin da ya kawo wadannan matsalolin a cewar rahoton, shi ne gazawa ce ta shugabanci tun daga karamar hukuma har zuwa matakin kasa.

Rikici a ko wane nau'in ya karu, sakamakon tu'amulli da kwayoyi, kamar yadda yawancin fursunonin ke shaidawa masu sa idon cewa samun kwaya abu ne mai sauki.

Haka kuma masu binciken sun gano wani zargin da ake wa jami'an gidan yarin kan yadda suke amfani da karfi, kuma ba wani kwakkwaran bincike da shugabannin gidan yarin suka gudanar.

Wasu jami'an gidan yarin na gallazawa fursunoni ta hanyoyin da suka saba wa dokokin gidan yarin kamar haramta ma su wanka a rana.

Akwai ayyukan kula da gidan yarin sama da 2,000, da ya kamata a ce an dauka amma shawarwari 22 daga cikin 89 ne kawai aka gabatar bayan rahoton 2015 da aka aiwatar.

Gazawar gwamnati

"Yana da wahala a iya fahimtar yadda shugabancin gidan yarin ya bari har matsalolin suka kai wannan matsayin," kamar yadda babban jami'in masu binciken ke kalubalar ma'aikatar shari'a.

"Mun samu kwararan hujjoji da suka tabbatar da jami'an gidan yarin sun nemi taimako daga hukumomi a matakin yanki har zuwa na kasa game da matsalolin da suka tabbatar da cewa ba za a lamunce ba kafin ziyararmu amma ba abin aka yi."

Rahoton ya kammala da cewa: "babu wani yunkuri da muka gani a kasa na tunkarar matsalolin."

Image caption Rahoton ya dora alhakin matsalolin ga shugabanni a matakin kananan hukumomi da yanki da ma kasa baki daya.

"Rahoto ne mafi muni da na taba gani," a cewar Lord Ramsbotham, tsohon babban sufeton gidan yari.

"Amma... ta yaya mutum zai zo daga hedikwata ya je Liverpool kuma ba zai ji kunya akai ba?"

"Ta yaya shugabannin gidajen yari suka bari har gidan yarin ya shiga irin wannan yanayin?"

An tambaye shi a kan rahoton, cewa Liverpool na iya zama gidan yari mafi muni a Ingila, Lord Ramsbotham ya amsa da cewa: "Ba zan karyata ba."

'Iyo cikin fitsari'

Wani fursuna da aka saki ya shaidawa BBC cewa: "Batun matsalar fama da kyankyasai abu ne mafi muni" za ka ji suna bibiyar ka da dare."

Sannan wani kuma ya ce yadda bututun ban-daki ya fashe, "Za ka ji kana iyo a cikin fitsari."

Image caption Darren Harley, daya daga cikin wadanda suka yi rayuwa a gidan yarin Liverpool

A lokacin bazara ne aka saki Darren Harley, bayan ya kwashe watanni 27 a gidan yarin kan laifin da ya shafi tu'ammuli da kwayoyi, ya danganta kuncin rayuwar da ya fuskanta a gidan yarin.

"Idan ka ajiye kare a wuri irin wannan, mutane za su zo su tafi da kai su rufe ka kan ka kuntatawa dabba."

"Mu mutane ne, don haka ya kamata a kula da mu da kyau."

Duk da ana danganta gidan yarin Liverpool a matsayin mafi muni, amma gidajen yari da dama a Ingila da Wales na fuskantar matsin lamba.

A karkashin gwamnatin hadaka, sakataren harakokin shari'a a lokacin, Chris Grayling ya datse yawan kasafin kudin gidajen yari da ma'aikata.

Tun datsewar, an samu karuwar kisan kai, da rikici da hare-hare a gidajen yarin.

Amincewa da gazawarta, ma'aikatar shari'a tana shirin daukar ma'aikata 2,500 a badi.

Cikin kwanaki kalilan an tube gwamnan gidan yarin Peter Francis bayan ziyarar, kuma a makon da ya gabata aka nada wani tsohon jami'in gidan yarin Pia Sinha a madadinsa.

A martanin da ta mayar kan gidan yarin Liverpool, Ma'aikatar shari'a ta ce: "Ba za mu yi magana kan wani rahoto da aka bankado ba"

Labarai masu alaka