Wadanne tambayoyi kuke da su a kan daukewar al'adar mace?

Mata na fuskantar matakai daban-daban

Asalin hoton, MARAMEDIA

Bayanan hoto,

Mata na fuskantar matakai daban-daban

Mata na hawa mataki-mataki a rayuwarsu, kamar tun daga haihuwa da 'yan matanci har zuwa girmansu da tsufansu.

A ko wanne mataki kuma su kan ci karo da al'amura daban-daban ko dai na sauyin tsarin halitta ko na rayuwa, kamar jinin al'ada da aure da haihuwa da raino.

Wani mataki da ke kawo sauyi sosai a rayuwar mace kuma shi ne na daukewar jinin al'adarta gaba daya, da kuma tsayawar haihuwa, wanda a turance aka fi sani da Menopause.

Sai dai akwai al'amura da dama da ke faruwa a wannan lokaci ga mace wadanda mata ba sa faye tattaunawa a kansu ba.

To ko wadanne tambayoyi kuke da su don karin haske a kan daukewar jinin ala'da? Kuna iya aiko wa da BBC tambayoyin, mu kuma za mu tuntubi likitoci don amsa muku su.