Boko Haram: Fayose zai ruga kotu kan $1bn

Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose

Asalin hoton, Twitter Fayose

Bayanan hoto,

Fayose ya ce kowace jiha tana fama da matsalolinta na tsaro

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya bayyana kin amincewa da matakin kashe dala biliyan daya daga rarar kudin fetir na Najeriya domin yaki da Boko Haram.

Fayose, ya ce jiharsa ta amince ya tafi kotu domin kalubalantar matakin.

Gwamnan ya fadi haka ne a wani taron gaggawa da gwamnonin suka gudanar a fadar shugaban kasa kan batun kashe kudaden rarar man da ya janyo cece-kuce a kasar.

A makon jiya ne kungiyar gwamnonin Najeriya, ta amince da matakin gwamnatin Tarayya na kashe dala biliyan daya daga kudaden rarar mai domin yaki da kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Gwamnoni 32 daga cikin 36 ne suka halarci zaman taron da aka amince da matakin tun da farko, kuma babu wanda ya nuna adawa.

Gwamnan Jihar Zamfara kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin Abdul'aziz Yari, ya ce sun amince da matakin ne bisa ra'ayin jam'iyyarsu da ke mulki.

Yari ya ce sun fahimci cewa sojoji na bukatar sabbin makamai, don haka a cewarsa bai kamata su yi wasa da batun tsaro fiye da sauran bukatu ba.

Gwamnan Ekiti wanda ba ya cikin taron da aka amince da bukatar tun da farko ya ce yana bukatar a ware wa jiharsa kudadenta daga kudaden na rarar mai.

Fayose, ya ce kowace jiha tana fama da matsalolinta na tsaro, sannan al'ummar jiharsa na cikin halin kunci, akan haka ya bukaci a bar ko wace jiha ta je ta ji da matsalolinta.

"Ina cike da kalubale, don haka su ba ni kudi na, Kudin jihar Ekiti ne", kamar yadda gwamnan ya shaida wa manema labarai bayan kammala taron gwamnonin.

Sauran gwamnonin dai sun amince a kashe kudaden dala biliyan daya duk da sun gaza biyan ma'aikatan jiharsu albashi.

Gwamnan Zamfara ya ce, amfanin kudin shi ne bacin rana kamar yanzu da ake kashe sojojin da ke fagen yaki da Boko Haram saboda rashin makamai duk da galabar da suke samu a kan mayakan.

Gwamnan ya ce an tsara yadda za a yi amfani da kudaden rarar man, ba wai za a kashe kudadn ba ne kawai a yaki da Boko Haram.

Boko Haram dai na ci gaba da zama barazana a arewa maso gabashin kasar, inda mayakan kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake tare da kashe fararen hula.