Dino Melaye ya fito a wakar hip-hop

Dan minsitan man Najeriya, Uche Kachikwu ya ce ba domin matsayin babansa ne Dino Melaye ya fito a bidiyonsa ba. Hakkin mallakar hoto Youtube/Uche Kachikwu
Image caption Dan minsitan man Najeriya, Uche Kachikwu ya ce ba domin matsayin babansa ne Dino Melaye ya fito a bidiyonsa ba.

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Dino Melaye, ya fito a bidiyon wata wakar hip-hop da dan karamin ministan man fetur na Najeriya.

A bidiyon mai tsawon minti uku da dakika 48 an nuna motoci na alfarma da lambar mota ta musamman mai dauke suna Dino.

An kuma yi ta watsa dalar Amurka dari-dari yayin da matan da suka yi shigar da ke nuna tsiraici suke rawa da maza.

Bidiyon dai da ya nuna kwarangwal na zinari da kuma mutane suna yi kamar suna cin dalar Amurka, kuma Dino ya fito daga wata mota sanye da riga da ke dauke da rubutu "Legend", wato gwarzo a harshen Ingilishi.

A makon jiya ne dai Sanata Dino Melaye ya wallafa kadan daga cikin bidiyon.

Tuni dai bidiyon ya fara jan hankalin 'yan Najeriyar, yayin da wasu suke yin Allah-wadai da bidiyon, wasu cewa suke wannan ba wata matsala ba ce.

Hakkin mallakar hoto Youtube/Uche Kachikwu
Image caption Habeeb Bombata ya ce: Na ga wannan fitowar ta Dino Melaye tun tuni, na gani a shafinsa na Instagram... ban ga wani abu mara kyau ba a nan.. dan ministan ya fitar da waka mai suna Dino kuma Dino ya fito a ciki
Hakkin mallakar hoto Twitter/@ogundamisi
Image caption kayode Ogundamisi ya ce: Dino Melaye yana nuna halin yawancin 'yan Najeriya ne wadanda suke ikirarin kyamar abin da ya yi. Yana nuna halinsu ne. Na daina tayar da hankalina kan maganar Najeriya.

Sai dai kuma mawakin da ya yi wakar, Uche, dan ministan man Najeriya, Ibe Kachikwu, ya ce sanatan ya fito ne a bidiyon domin ya ba shi karfin gwiwa.

Ya ce: "Ba wai ya fito da mata ko kuma ba wai ya wakilci Najeriya ba ne a bidiyon."

Hakkin mallakar hoto Youtube/Uche Kachikwu
Image caption Sanata Melaye dai ya wallafa kadan daga cikin wakar a shafinsa na Instagram a makon jiya

Mawakin dai ya musanta cewa mukamin babansa ne ya sa Sanata Melaye ya fito a bidiyon, yana mai cewa shi ya tsani a hada cigabansa a fagen waka da mukamin babansa.

Labarai masu alaka